✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NDLEA ta kama babban limami da kunshin wiwi 54 a Legas

Limamin ya ce zai je kasar Kenya ne aikin da’awa tare da kayen mayen.

Hukumar da ke Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA) ta ce ta na ci gaba da gudanar da bincike bayan ta kama wani babban limamin coci da kunshin tabar wiwi 54.

A cewar NDLEA ta kama Rabaran Ugochukwu Emmanuel limamin cocin Christ Living Hope a filin jirgin sama na Murtala Muhammad a Legas a makon jiya.

Bayanai sun ce limamin ya shiga hannu ne yayin da ake binciken fasinjoji inda aka gano ya nannade wasu kunshin kayan maye a jikinsa.

Rabaran Ugochukwu ya bayyana cewa zai je Nairobi, babban birnin kasar Kenya ne aikin da’awa tare da abubuwan.

Mista Femi Baba Femi, kakakin hukumar NDLEA mai yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya ya shaida wa manema labarai cewa “a yayin da ake bincikensa an gano wasu abubuwa guda 54, kuma daga baya aka tabbatar da cewa tabar wiwi ce.”

Baba Femi ya ce a halin yanzu ana ci gaba da bincike kan dalilin yin hakan, domin samun wasu shaidun da ke tabbatar da cewa ko ba fataucin miyagun kwayoyi yake yi ba.