✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

NDLEA ta kama dilolin kwaya 100, ta fasa dabar shaye-shaye 14 a Kaduna

An dilolin kwaya maza da mata sun shiga hannu a garin Zariya da kuma Kaduna

Dillalan miyagun kwayoyi guda 100 sun shiga hannu, a yayin da aka tarwata matattarar masu shaye-shaye 14 a Jihar Kaduna a cikin mako hudu da suka gabata.

Kwamandan Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA) a Jihar Kaduna, Umar Adoro, ya ce dillalan miyagun kwayoyin da jami’an hukumar suka kama sun hada da maza 93 da mata bakwai.

Ya bayyannan cewa an kama dilallan miyagun kwyoyin da kuma tarwatsa wuraren da ake shaye-shayen ne a samamen da hukumar ta kai a garin Zariya da kuma Kaduna a cikin wata Mayu da ya gabata.

Ya ce bayyana cewa unguwannin da aka tarwatsa matattarar masu shaye-shayen miyagun kwayoyin sun ha hada da Abakwa da Malali da Tirkaniya da Rigasa da Romi da Filin Misata a garin Kaduna.

Sai kuma unguwannin Chikaji da Sabon Gari da sauransu da ke Karamar Hukumar Zariya.