✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NDLEA ta kama hodar iblis mai nauyin kilo 394 a Taraba

NDLEA ta bukaci karin cibiyar gyaran hali a jihar.

Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA), ta cafke wasu mutum takwas da hodar iblis mai nauyin kilo 394.415 a Jihar Taraba.

Kwamandan Hukumar a Jihar, Jadi Suleiman ne ya bayyana hakan yayin taron da ka gudanar na bikin Ranar Yaki da Shan Miyagun Kwayoyi ta Duniya.

  1. ‘Matawalle ya sauya sheka daga PDP zuwa APC’
  2. Buhari ya nada Obinna a matsayin sabon Shugaban PPPRA

Ya ce an cafke wadanda ake zargin a tsakanin watan Janairu zuwa Yunin wannan shekara da suka hada da mutum takwas da ake yanke wa hukunci da kuma wasu 135 da ke jiran na su hukuncin daga kotu

Mista Suleiman ya ce an samu tsaiko wajen yanke musu da hukunci sakamakon yajin aikin da Ma’aikatan Shari’a suka yi na tsawon watanni biyu.

Kazalika, ya tabbatar da cewar ana sa ran samun wasu da dama da za su amsa laifukansu tunda kotuna sun dawo bakin aiki.

Ya ce, hukumar ta gudanar da gangamin wayar da kan a’umma game da illar shaye-shaye ke haifarwa a makarantu, kasuwanni, tashoshin mota, asibitoci da sauran wurare.

Sai dai ya bayyana rashin aikin yi a tsakanin matasa a matsayin abin da ke haifar da shaye-shaye a wannan kasar.

A cewarsa, cikin mutum miliyan 10 da ke Najeriya, kashi 80 cikin 100 da ke shaye-shaye matasa ne ’yan tsakanin shekara 19 zuwa 45.

Har wa yau, ya bukaci samar da karin cibiyar bayar da horo da kuma gyaran hali a Shelkwatar hukumar da ke jihar ta Taraba.

Ya ce Jihar Taraba ba ta cin moriya shirye-shiryen da ake gudanarwa a wasu jihohi sakamakon rashin cibiyar gyaran hali da take da shi.