NDLEA ta kama hodar iblis ta N2.7bn a filin jirgin saman Abuja | Aminiya

NDLEA ta kama hodar iblis ta N2.7bn a filin jirgin saman Abuja

Kunshin wata Hodar Iblis da NDLEA ta kama
Kunshin wata Hodar Iblis da NDLEA ta kama

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA), ta kama kilo 9.30 na hodar iblis da darajarta ta haura Naira biliyan 2.7 a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.

Cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, Kakakin NDLEA na Kasa, Femi Babafemi, ya ce an kama hodar iblis din ce a hannu wani matashi mai shekaru 32 da haihuwa mai suna Maduabuchi Chinedu.

Mista Babafemi ya ce wanda ake zargin wanda dan asalin kauyen Obaha Okigwe ne a Karamar Hukumar Okigwe ta jihar Imo, yana zaune ne a kasar Laberiya inda yake aikin hakar ma’adinai.

Ya ce an kama wanda ake zargin ne a wani binciken hadin gwiwa a jirgin Ethiopian Airlines mai lamba 911 a filin jirgin Abuja a ranar 24 ga watan Nuwamba.

Ya ce matashin ya kunshe hodar iblis din mai nauyin kilo 9.30 da ya nannade cikin wani kwanson alawa da aka boye a cikin jakunkunan matashin.

Sai dai Mista Babafemi ya ce matashin ya ce matsin rayuwa ya sanya ya shiga wannan harka da aka dora shi a kanta a kokarin da yake na ganin ya tara kudin maganin matsalar ciwon ido da mahaifiyarsa take fama da shi.

Kazalika, Mista Babafemi ya ce Shugaban Hukumar NDLEA na Kasa, Birgediya Janar Buba Marwa mai ritaya, ya yaba wa kwazon jami’an hukumar da kuma jami’an hukumar leken asiri ta NIA bisa fadi-tashin da suke yi tare da sauran hukumomin tsaro a filin jirgin saman wajen cafke masu fataucin miyagun kwayoyi.