✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NDLEA ta kama Kwayar Tramadol ta N8.8bn a Legas

Jami'an NDLEA sun kama kwayoyi sama da miliyan 13 da dubu 452 na Tramadol da kudinsu ya kai N8.9b

Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA) ta gano kwayoyin Tramadol guda sama da miliyan 13 da dubu 452 da kudinsu ya kai Naira bilyan 8.9 a Jihar Legas.

Daraktan Yada Labarai na Hukumar, Femi Babafemi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin a Abuja.

Babafemi ya ce jami’an NDLEA sun kuma kama wanda ake zargin shi ne dillalin miyagun kwayoyin wanda aka gano a cikin kwalaye 443.

Ya ce ma’aikatan Hukumar sun kama kwayoyin Tramadol din a wani katafaren gidan wanda ake zargin ne a unguwar Victoria Garden da ke Lekki a Jihar.

Ya ce kamen mutumin, wanda shugaban wani kamfanin sayar da motoci ya zo ne wata biyu bayan NDLEA ta gano wani dakin hada kwayar methamphentamine, mamallakin wani dillalin kwaya a unguwar, wanda aka kama tare da wanda ke hada masa kwayar.

Babafemi ya ce kafin kama shi, mutumin na cikin jerin wadanda Hukumar reshen Ihiala ta ke bibiyar motsinsa.

Wanda ake zargin dai ya ce yana daya daga cikin manyan masu safarar miyagun kwayoyin Tramadol a Najeriya.