✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NDLEA ta kama mai kai wa ’yan bindiga kwayoyi da albarusai

An dai kama mutanen ne suna kokarin tsallakewa da kwayoyi da albarusai.

Jami’an Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) sun kama ‘sojan karya’ da ke yi wa ’yan bindiga safarar miyagun kwayoyi da albarusai.

Dubun mutumin, mai suna Hayatu Galadima da abokin harkar shi, Hamisu Adamu ta cika ne lokacin da yake kokarin kai wa ’yan bindigar kwayoyin da kuma albarusai.

Jami’an hukumar da ke sintiri a kan babbar hanyar Gwagwalada ne suka cafke su ranar Juma’a.

Kakakin hukumar, Femi Babafemi a cikin wata sanarwa ranar Lahadi ya ce an kama su da kayayyaki da dama.

“Kayan da muka kwace daga hannunsu sun hada da wasu albarusai guda 21 da aka boye a robar ruwa, fakiti 16 na kwayar ‘Walkie talkie’, hulunan silke na sojoji guda hudu, lalita mai dauke da ID card din sojoji, Dalar Amurka daya da kuma katunan ATM guda shida na bankunan FCMB da First Bank da UBA da kuma Skye.”

Kazalika, kakakin ya ce an kuma kama kullin tabar wiwi, kwayoyin Tramadol, layukan waya na MTN guda uku da na 9mobile guda biyu, sai kuma na Airtel guda daya, da wayar salula kirar iPhone 12 pro da Samsung A31 da Nokia guda daya da takardun izini na sojoji guda bakwai da kuma wata ledar ‘Gari-ya-dau-zafi’ dauke da suttura da kuma galan din manja.

Sanarwar ta ce yayin da Hayatu Galadima ya yi ikirarin shi soja mai mukamin Lance Corporal da ke aiki a Ibadan, sun ce suna kokarin kai kayan ne zuwa Kano da Kaduna.

“Amma bincikenmu ba farko-farko ya nuna cewa akwai yuwuwar suna kokarin kai kayan ne ga ’yan bindigar da ke Jihohin Arewa maso Yamma, bayan an katse hanyoyin sadarwa a Zamfara da Sakkwato da Kaduna,” inji Babafemi.

Ya ce tuni shugaban hukumar, Birgediya Janar Buba Marwa (mai ritaya) ya ba da umarnin a mika wadanda ake zargin ga sojoji wadanda dama sun taba ayyana nemansu ruwa a jallo.