✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NDLEA ta kama sarakai suna shaye-shaye a Jigawa

An kama sarakunan dumu-dumu a matattarar shan miyagun kwayoyi.

An kama wasu masu rike da sarautun gargajiya a yayin da suke tsaka da shaye-shaye a matattarar masu shan miyagun kwayoyi a Jihar Jigawa. 

Jami’an hukumar Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA) sun ritsa sarakan su biyu da wasu ’yan siyasa biyu ne a yayin wani samame a matattarar masu shaye-shaye a sassan jihar.

A lokacin samamen, jami’an hukumar sun cafke mutum 134 masu ta’ammali da miyagun kwayoyi, ciki har da mata biyu da kuma dalibai 25 da ke karatu a manyan makarantun jihar.

Kwamandar NDLEA a Jihar Jigawa, Maryam Gambo, ta ce dubun sarakunan da sauran mutanen ta cika ne a yayin samamen da suka kai wa matattarar masu shaye-shaye daban-daban a sassan jihar daga ranar 27 ga watan Satumba zuwa 10 ga watan Oktoba, 2021.

Duk da cewa ta ki ta bayyana sunayen sarakan, ta ce, “Wuraren da muka kai samamen a Dutse sun hada da garejin tifa, Maranjuwa da kuma kwanar Yalwawa.

“A Hadejia kuma mun kai samame a Gandun Sarki, Salbas, Sawaba da sauran wurare.”

Ta ce kayan shaye-shaye da aka kwace daga hannun mutanen sun hada da tabar wiwi da kuma kwayoyi.

A lokacin da take gabatar da su a ofishin hukumar da ke Dutse, Kwamanda Maryam, ta ce hukumar za ta yi amfani da bayanan da ta samu daga wadanda ake zargin domin kamo dillalen miyagun kwayoyi a jihar.