✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NDLEA ta kama ’yan kwaya 78 da kilogiram 113 na kwayoyi a Sakkwato 

Hukumar Yaki da sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta kama ’yan kwaya 78 da kilogiram 113 na miyagun kwayoyi daga watan Janairu…

Hukumar Yaki da sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta kama ’yan kwaya 78 da kilogiram 113 na miyagun kwayoyi daga watan Janairu kawo wannan lokacin a Jihar Sakkwato.

Kwamandar hukumar a Jihar, Iro Muhammad ne ya bayyana hakan a wani taron da manema labarai, don murnar zagoyowar bikin ranar yaki da sha da fataucin kwayoyi da aka gudanar ranar Talata.

Ya ce cikin kayan mayen da hukumar ta gano, akwai kilo gram 91 na Tabar Wiwi da wasu magunguna ciki har da Kodin da suka kai lita 63.

Ya kuma ce hukumar ta sami nasarar gurfanar da mutum 12 a tsakanin wannan lokacin, hadi da horar da ’yan kwaya 58 da ‘yan uwansu suka kawo su don gyaran hali.

Kwamandan ya kuma ce manufar bikin ita ce wayar da jan al’umma kan illolin shan miyagun kwayoyi.