✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NDLEA ta kama ’yan mata masu dillancin kwayoyi

An bankado gidan da ake ajiye 'yan mata suna karuwanci da sayar da kwayoyi.

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta bankado wani otal da ake hada-hadar miyagun kwayoyi tare da ajiye ’yan mata suna karuwanci a Abuja.

NDLEA ta kama mata uku da namiji daya suna shan hodar ibilis a otal din mai suna JAT Suites da ke unguwar Wuse 2, inda hukumar ta kama miyagun kwayoyi da dama a ranar Laraba da ta gabata.

Kakakin NDLEA na kasa, Femi Babafemi, ya ce hukumar ta gano cewa otal din ba shi da rajisata kuma ‘gagararrun ’yan mata’ na taruwa a nan suna sha da sayar wa ’yan mata da kwastomomin otal din kwayoyi.

Ya ce Shugaban NDLEA, Birgediya Mohamed Buba Marwa (mai ritaya), ya umarci ofishin hukumar na Abuja ya bi duk hanyoyin da suka dace a hukumance don ganin an mallaka wa gwamnati ginin otal din domin hakan ya zama izina ga masu irin muguwar dabi’a.

Babafemi ya ce hukumar ta kuma kama wata mata a filin jirgin sama na Murtala Mohammed da ke Legas, tana kokarin fitar da kwayar Kodin mai nauyin kilogram 15.15kg zuwa kasar Birtaniya; an kuma kama wani mutum da kwalaben Kodin masu nauyin kiligram 5.65.

Akwai kuma kwayar Tiramol mai nauyin kilogram 150.30 da aka kama a ranar Litinin 20 ga Satumba, 2021.

Hukumar ta kuma kama wasu dalibai mata biyu da ke karatu a Kwalejin Kimiyya da Kere-kere ta Jihar Edo, a ranar 23 ga Satumba, 2021 dauke da kulli 21 na tabar wiwi, washegari kuma aka kama wata mata dauke da hodar iblis mai nauyin giram 200 a wani gidan abinci a garin Benin.

A ranar ce kuma aka kwace bahu 10 na tabar wiwi mai nauyin kilogram 135  a dajin Amahor da ke Jihar Edo, a daidai lokacin da dilolinsu ke shirin kai su sassan Najeriya.

A Jihar Kaduna kuma an kama wata mata da mijinta ya rasu, wadda kasurgumar dilar tabar wiwi ce.

An kama ta ne da tabar wiwi mai yawan gaske a kauyen Afana da ke Karamar Hukumar Zango Kataf za ta kai tabar wiwin zuwa Jos.

A baya an taba daure ta na tsawon wata shida a gidan yari bayan an kama da tabar wiwi mai nauyin kiligram 45 a watan Maris na shekarar 2020.