✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NDLEA ta lalata miyagun kwayoyi na N50bn a Abuja

Hukumar ta ce yawan kwayoyin da aka lalata ’yar manuniya ce kan girman matsalar a Najeriya.

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta lalata kilogiram 20,000 na miyagun kwayoyi wanda darajarsu ta kai kusan Naira biliyan 50 a Abuja.

Shugaban hukumar, Birgediya Janar, Buba Marwa (mai ritaya) ne ya sanar da hakan lokacin da ake kona kwayoyin a Abuja ranar Talata.

Ya ce yanzu haka hukumar na fuskantar garambawul, lamarin da ya sa take samun gagarumar nasara.

Buba Marwa, wanda ya samu wakilcin Sakataren hukumar, Barista Shadrach Haruna, ya kuma ce yawan kwayoyin da aka lalata ’yar manuniya ce kan girman matsalar ta’ammali da miyagun kwayoyi a Najeriya.

Ya ce, “Kwayoyin da muka lalata yau sun kai kilogiram 20,000, kuma darajarsu ta kai sama da Naira biliyan 50.

“A kiyasce, kilogiram 19,598 na kwayoyin reshen rundunarmu na Babban Birnin Tarayya Abuja ne ya kwace su, ciki har da kilogiram 19,178 na Tabar Wiwi, kilogiram 0.1 na Hodar Iblis da kuma kilogiram 420 na sauran miyagun kwayoyi.

“Sauran kwayoyin da muka kwace a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja sun hada da kilogiram din Hodar Iblis, kilogiram 36 na Wiwi, 93 na kwayar ephedrine, kilogiram 60 na methamphetamine, sai giram 219 na Rohypnol da kuma giram 150 na kwayar Tramadol,” inji shi.

Buba Marwa, ya kuma ba da tabbacin hukumar na ci gaba da hada gwiwa da dukkan masu ruwa da tsaki, ciki har da masu rike da sarautun gargajiya da shugabannin addini da na al’umma don kawo karshen matsalar.