Daily Trust Aminiya - NECO ta fitar sakamakon jarabawar 2020
Subscribe

NECO ta fitar sakamakon jarabawar 2020

Hukumar Shirya Jarabawa ta Najeriya (NECO) ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare da aka rubuta a 2020.

NECO ta kuma soke sakamakon jarabawar wasu makarantu 12 ta kuma sanya musu takunkumin shekara saboda kama su da aikata magudin jarabawa.

Shugaban Hukumar, Farfesa Godswill Obioma ya ce makarantun da aka soke sakamakon jarabawarsu sun hada da “4 da Jihar Adamawa, Jihar Kauduna 2, Jihar Katsina 2, Jihar Neja 2, Jihar Taraba 1 da kuma 1 a Abuja, kuma hukumar ba za ta kara hulda da su ba sai bayan shekara biyu.”

Farfesa Obioma ya bayyana cewa dalibai 33,470 ne aka soke jarabawarsu saboda magudin jarabawar da aka yi a makarantun guda 12.

Shugaban na NECO ya kara da cewa Hukumar ta kuma dakatar da jami’an sanya ido aka jarabawa 24 su saboda samun su da laifukan magudi.

Ya ce laifukan da aka kama su da shi sun hada da taimakawa da kuma ba da hadin kai ta hanyar barin baki su rubuta wa dalibai jarabawa, ko ma a rubuta wa dalibai amsar jarabawa a kan alluna.

Sai dai ya ce duk da haka, magudin jarabawar da aka samu a 2020 ta ragu idan aka kwatanta da dalibai 40,730 da aka kama a jarabawar 2019.

A cewarsa, nasarar ta samu ne saboda amfani da fasahar daukar bayanai da kuma tantance dalibai na zamani da kuma inganta tsarin jarabawar da hukumar ta yi.

More Stories