✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NEDC ta raba wa tubabbun ’yan Boko Haram kayan abinci a Borno

NEDC ta ce tilas ne a ci gaba da tallafa wa wadanda ta'addancin Boko Haram ya rutsa da su.

Hukumar Raya Arewa maso Gabas (NEDC), ta bayar da tallafin kayan abinci a raba wa tubabbun ’yan Boko Haram kusan 66 da iyalansu da sauran wadanda rikicin ta’addanci ya shafa a Jihar Borno.

Da yake mika kayan tallafin ga gwamnatin Jihar Borno a ranar Asabar, Shugaban NEDC, Alhaji Mohammed Alkali ya bayyana cewa, an raba kayan abinci ne domin tallafa wa ayyukan sake tsugunar da ‘yan gudun hijirar da ake yi a jihar.

Alhaji Alkali ya kara da cewa, sannu a hankali zaman lafiya ya soma dawowa yankin Arewa maso Gabas kuma gwamnatin jihar na iyaka bakin kokarinta wajen sake tsugunar da ‘yan gudun hijirar da ‘yan tada kayar bayan suka raba da muhallansu.

Da yake jawabi a ranar Asabar, Shugaban na NEDC ya ce wajibi ne hukumar ta taimaka wa yankin Arewa maso Gabas a shirin tsugunar da jama’a, wanda wani yunkuri ne sake gina yankuna da al’ummomin da ‘yan tada kayar bayan suka rusa a baya.

Ya kara da cewa, duk da cewa Gwamnatin Tarayya ta kafa wani kwamitin da zai tabbatar da dawowar ‘yan gudun hijira da tubabbun ‘yan tada kayar bayan, amma hukumar ta ga ya dace ta samar da agajin jin kai ga wadanda ke sansanonin da kuma sabbin mutanen da aka sake tsugunar da su.

“Mun ga ya zama dole a taimaka wa gwamnatin jihar wajen samar da wasu abubuwan jin dadin rayuwa ta fuskar abinci domin wadanda ke kusa musamman wadanda ke sansanonin da wadanda suka koma yankinsu ko kuma suka sake tsugunar da su a wani wuri kafin a taimaka.

“Mun ga ya dace a ci gaba  tallafa wa kokarin da Gwamnatin Tarayya da Gwamnatin Borno a kokarin da suke yi na kula da ’yan gudun hijirar da kuma tubabbun ’yan kungiyar Boko Haram.”

Shugaban na NEDC ya kuma bayyana cewa hukumar ta sayo kayan abincin ne daga wani kamfanin sarrafa abinci a kokarin farfado da masana’antu masu fama da rashin kula a yankin da hakan ke barazana ga durkushewar su dungurungum.

A jawabinta lokacin da take karbar kayayyakin a madadin gwamnatin Jihar Borno, Darakta Janar ta Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Borno (SEMA), Hajiya Yabawa Kolo, ta gode wa NEDC bisa wannan tallafin.

Hajiya Kolo ta bayar da tabbacin cewa shirye-shirye tuni sun yi nisa wajen sake tsugunar da wadannan  ‘yan gudun hijirar tare da kokarin mayar da su zuwa gidajensu na asali.

Ta jaddada cewa gwamnatin jihar ta dukufa wajen ganin an dawo da dawwamammen zaman lafiya a Jihar Borno da ma yankin Arewa maso Gabas baki daya.

Aminiya ta ruwaito cewa, daga cikin kayayyakin abincin da aka bayar tallafi sun hada da buhuna 10,000 na shinkafa mai nauyin kilo 25, buhunan masara 10,000, katan-katan na taliya guda 4,000, man girki galan 4,000, barguna 5,000 da katifun roba 5,000 da sauransu.