✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Nelson Mandela ya mutu da fushin Najeriya

Na dade a rayuwata da burin ganawa da Mandela kuma na samu damar yin haka a 2007, kodayake ban samu haka da sauki ba.Farkon haduwar…

Na dade a rayuwata da burin ganawa da Mandela kuma na samu damar yin haka a 2007, kodayake ban samu haka da sauki ba.
Farkon haduwar tamu, tambayar da ya fara yi mini ita ce: “Yaya ’yan uwana maza da mata na Najeriya?” Kafin ma in fara ba shi amsa, sai ya ci gaba da cewa: “Ka san fa cewa ina kullace da Najeriya, ina fushi da ita. Nakan nuna haka a wurare daban-daban kuma sau da dama.”
Daga nan na zaku in ji abin da ya haifar da haka, kodayake ina sane da cewa shi ne kanwa uwar gamin da ya sanya aka dakatar da Najeriya daga kungiyar kasashe Rainon Ingila (Commonwealth), saboda kin amincewa da sarkafe Ken Saro Wiwa da danginsa ’yan yankin Ogoni. Haka kuma ina sane da cewa gwamnatin kasarsa, Afrika Ta Kudu ta dade tana dari-dari da Najeriya, musamman ma a lokacin da na ziyarce shi, sunan Najeriya abu ne abin ki a kasar tasu.
Na shaida masa cewa al’ummar Najeriya suna lafiya kuma suna yi wa al’umar Afrika Ta Kudu fatan alheri, sai dai suna matukar mamakin yadda ake kyara da kyamatar su a kasarsa, duk kuwa da cewa sun jajirce, sun ba da tallafi sosai wajen samar masu da ’yanci.
“kwarai kuwa,” iniji Mandela. “Najeriya ta taya mu alhini, ta tallafa mana fiye da kowace kasa amma kun lalatar da kanku, kun kunyatar da Afrika da al’ummar bakaken fata na duniya.”
Ganin cewa Mandela ya shirya yi mini cikakken bayani, sai na kara kintsawa, na gyra zama, na saurare shi. Ya bayyana mani irin bakin ciki da takaicinsa game da Najeriya, kasar da ke dauke da mafi yawan bakaken fatar duniya, kasar da Allah Ya ba albarkar jama’a da dukiya da albarkatun kasa, wadanda ya kamata a yi amfani da su wajen bunkasa ta a duniya amma ta zama wani wuri wulakantacce, inda ake kyankyashe tsagwaron kasurguman masu laifi da tantiran shugabanni masu danne talakawa.
Ya ci gaba da bayyana mani cewa, al’umma na daratta Najeriya, domin kuwa bayan da aka dakatar da ita daga kungiyar kasashe Rainon Ingila, wasu da dama daga kasashen Yammacin Duniya sun tuntube shi, suka ce ya taimaka domin a samu damar karya shugabannin mulkin soja, ’yan-kama-karya a Najeriya. Kamar yadda ya ce: “Na tuntubi kasashen Afrika da dama kan haka amma suka shaida mani cewa lallai in kiyayi Najeriya, za ta iya gyara al’amuranta da kanta, domin kuwa ta taba fuskantar irin wannan matsala. Amma abin takaici, a wannan karon kun gaza. Duniya ba za ta taba girmama Afrika ba har sai idan Najeriya ta mutunta kanta. Al’ummar bakaken fata na duniya suna son ganin Najeriya ta bunkasa a duniya, domin kuwa ita ce abin tokabo da alfaharinsu. Kuma ina sane da cewa ’yan Najeriya suna son ’yanci, ba su son danniya da zalunci. Amma me ya sanya kuke zaluntar kanku?” Ya kara da cewa yakan tuna Tafawa balewa, Shugaban Najeriya na farko, wanda ya ba jam’iyyarsa, ANC gudunmowar kudi.
A nan ne na samu damar bayyana masa cewa, ai ba Najeriya ce kadai ke da irin wadannan shugabanni ba azzalumai, kusan dukkan shugabannin kasashen Afrika, haka suke. Haka kuma, na ce ya yi hakuri, hatta shugabancinsa a Afrika Ta Kudu, bai kawo wa bakaken fatar kasarsa wani canji na a zo a gani ba kuma babu alamar cewa magadansa za su yi haka.
“Batunka gaskiya ne,” inji shi. “Amma mun tallafa wa wasu, mun sanya masu karsashi, don haka za su iya kawo canji nan gaba. Amma ku a Najeriya, shugabanninku ba su mutunta al’ummarsu, sun fi kyautata wa kansu, domin suna ganin cewa idan abin da suke so, shi ne talakawansu suke so. Sukan kwashe dukiyar al’umma su saka aljifansu. Talauci ya yi katutu a Najeriya, kuma bai kamata a amince da haka ba. Ni dai ina mamakin ’yan Najeriya yadda suke nuna hakuri kan haka. Ya kamata a ce suna nuna fushi fiye da yadda suke nunawa.”
Da na lura da cewa tsohon nan dai yana dauke da bayanai masu yawa game da Najeriya, sai na kara ara masa kunnuwa, ya ci gaba da amayar da bayaninsa: “Ko yaya matasan Najeriya ke daukar shugabanninsu, wane tunani suke yi game da Najeriya da Afrika? Kuna koyar da su tarihi, ko kuwa kuna koya masu darussan tarihi? Misali, kuna sanar da su yadda shugabanninku na farko suka ba mu tallafin kudi masu yawa? Ka san na ji daga bakunan ’yan Zimbabwe da ’yan Muzambik da ’yan Angola, yadda mutanenku suka taimaka masu. A lokacin nan ina garkame a jgidan jarun amma dai ina sane da yadda shugabanninku suka ladabtar da shugabannin kasashen Yammacin Duniya da suka ba da goyon baya ga wariyar launin fata.”
Na tunasar da shi cewa muna kan mulkin dimokradiyya tun daga 1999 kuma ya san wasu daga cikin shugabanninmu sosai. Ya ce: “Haka ne amma yaya batun cin hanci da rashawa da sauran laifuffuka daban-daban? Salon yadda kuke gudanar da zabe ya yi kama da yadda ake fafata yaki. Yanzu ma na ji ana cewa wai mutum ba zai zama Shugaban kasa ba sai har in ya kasance shi Musulmi ne ko Kirista. Wasu ma sun shaida mani cewa wai kasarku za ta rabu, to kada ku sake ku bari haka ta faru.”