✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Neman aiki: Nakasassu sun yi wa AMCON zanga-zanga

Kungiyar nakasassu na neman a dauke su aiki a hukumar kuda da kadarori ta AMCON

A yunkurinsu na ganin ana damawa da su, nakasassu sun yi zanga-zangar lumana a Ofishin Hukumar da ke Kula da Kadarori ta AMCON, domin hukumar ta rika daukar su aiki.

Wakilan kungiyar ta masu bukatar karkashin jagorancin Shugabanta Mista Godstime Onyegbulam, ya ce sun zo hedikwatar hukumar ne domin su nuna mata bukatarsu ta duk lokacin da za ta dauki ma’aikata ta dauki ’ya’yan kungiyar wadanda suka cancanta.

A wani jawabinsa ga hukumar Onyegbulam, ya ce sun san AMCON hukuma ce mai bin doka da oda sannan akwai kadan daga cikin masu bukata ta musamman da suke aiki a hukumar amma sun yi kadan.

A lokacin da suke yi wa ’yan kungiyar bayani, wakilan hukumar ta AMCON Alhaji Mamuda Shehu da Mista Albert Nwanozie, sun bayyana wa masu zanga-zangar cewa daga cikin ma’aikatan hukumar tana da wadanda suke da bukata ta musamman.

Sun kuma ce hukumar za ta ci gaba da ba wa duk ’yan Najeriya dama ba tare da nuna wariya ba domin duk ’yan Najeriya suna da tasu gudunmuwar da za su bayar wajen cigaban kasa.