✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Neman gurbin AFCON: Najeriya ta lallasa Sao Tome and Principe da ci 10-0

Dan wasan Najeriya Osimhen shi kadai ya ci kwallo hudu

A ci gaba da buga wasannin neman cancantar buga kofin nahiyar Afirka (AFCON), tawagar Najeriya ta Super Eagles ta lallasa takwararta ta Sao Tome and Principe da ci 10 ba ko daya.

A wasan dai wanda aka fafata ranar Litinin, dan wasan Najeriya Victor Osimhen ne ya ci wa Super Eagles kwallo hudu shi kadai.

Osimhen ya fara zura wa Najeriya kwallo ta farko ne a minti na tara da fara wasan, kafin ya taimaka wa Moses Simon da Terem Moffi su ma su zura nasu kwallayen a mintuna na 28 da na 43.

Ya kuma kara kwallonsa ta biyu a ragar abokan hamayyar nasu a minti na 48, sannan ya kara ta uku a minti na 65.

Osimhen, wanda dan wasan gaba ne a kungiyar kwallon kafa ta Napoli da ke kasar Italiya ya ci kwallonsa ta hudu ne a minti na 84, lamarin da ya kawo adadin kwallayen da Najeriya ta ci zuwa biyar.

Shi kuwa Terem Moffi ya ci kwallonsa ta biyu ne a minti na 60, sai Oghenekaro Etebo da Dennis Emmanuel da kuma Lokman Ademola su ma suka zuzzura kwallo dai-daya.