✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Neman Saki: Sadakin aure kadai za mu mayar — Lauyan Balaraba Ganduje

'Yar gwamnan na Kano ta dage kan mijin nata ya sake ta.

Barista Ibrahim Aliyu Nassawara, lauyan da ke wakiltar ’yar Gwamnan Jihar Kano, Hajiya Asiya Balaraba Ganduje, ya shaida wa Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke zamanta a Filin Hoki a jihar cewa, sadakin Naira dubu 50 kadai za su mayar wa mijin Balaraba.

Wannan ya biyo bayan sharadin da lauyan mijin Balaraba Ganduje wato Alhaji Inuwa Uba, ya gindaya wa bangaren masu kara, inda ya ce bayan sadaki na Naira dubu 50 da suka biya suna kuma bukatar mai kara ta dawowa da mijnta wasu kayayyakinsa da ke hannunta.

A cewar Barista Umar I. Umar, akwai wasu motocinsa a wajenta da takardun karatunsa da kuma takardun kadarorinsa da suka hada da na gidaje da sauransu.

Daga cikin sharudan nasa ya nemi matar tasa ta sarayar da hakkinta na hadakar da suka yi wajen kafa wani kamfanin shinkafa.

“Idan tana bukatar ta fanshi kanta to ba maganar dawo masa da sadakinsa na naira dubu 50 ba ne kadai.

“Muna bukatar ta dawo masa da sauran kayayyakinsa da suka hada da takardun karatunsa da kuma takardun kadarorinsa.”

Sai dai a martanin da suka mayar lauyoyin mai kara karkarshin jagorancin Barista Ibrahim Aliyu Nassarawa, ya ce “Ba a yin khul’i a kan abin da yake a wajen aure.

“Wannan kaya da yake da’awa ba su shafi khulu’i ba.

“Shi khulu’i ana yinsa ne a kan abin da aka jingina aure a kansa musamman sadaki amma ba wai a kan wani abu na daban ba.”

A cewar Barista Nassarawa, sadakin Naira dubu 50 za su mayar wa wanda ake kara.

“Kamata ya yi idan an kammala wannan shari’a sai ya nemi hakkinsa ta hanyar shigar da wata kara daban a kuma wata kotun ta daban.

“Amma mu a yanzu abin da muka sani shi ne Naira dubu 50 kuma shi kadai za mu biya.”

Bayan tafka zazzafar muhawara, dukkannin bangarorin biyu sun ki amincewa da juna.

Alkalin kotun Mai Shari a Khadi Abdullahi Halliru, ya ayyana 2 ga watan Fabrairu 2023 a matsayin ranar yanke hukunci.

Idan za a iya tunawa dai ‘yar gwamnan Kano, Asiya Balaraba Ganduje ce ta shigar da karar, inda ta nemi kotun ta datse igiyar aurenta na shekara 16 da mijinta, Alhaji Inuwa Uba.

Balaraba Ganduje ce dai ta shigar da karar mijin nata, tana rokon kotun ta raba aurensu ta hanyar Khulu’i, saboda ta gaji da zama da shi.

Sai dai mijin nata Inuwa Uba ta bakin lauyansa Barista Umar I Umar, ya ce sun yi iya kokarinsu na son ganin matar tasa kuma uwar ’ya’yansa guda hudu ta dawo dakinta amma abin ya ci tura.