✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ni ba dan takarar Arewa ba ne —Ahmad Lawan

Ahmad Lawan ya ce yana neman kujerar shugaban kasa ne saboda yana da duk kwarewar da ta dace ya da kujerar

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ya ce ba a matsayin dan takarar yankin Arewacin Najeriya fito neman kujerar shugaban kasa ba.

Ahmad Lawan ya ce yana neman kujerar shugaban kasa ne saboda ya yi amanna yana da duk kwarewar da ta dace ya zama shugaban kasar Najeriya domin dorawa a kan bagarorin da ta samu nasarori.

“Ba fitowa na yi a matsayin dan takarar yankin Arewa ba kamar yadda ake yadawa, ko yadda wasu ’yan Arewa ke cewa ba za a ba wa yankin Kudu mulki ba.

“Na fito ne kamar kowane dan takara dan Najeriya, na fito ne da duk irin kwarewar da nake da ita, don haka sai mutane su yi min alkalanci bisa hakan,” inji shi.

Ya bayyana haka ne a lokacin ziyarar da ya gana da ’yan jam’iyyarsa ta APC, musamman daliget a Jihar Katsina, a ranar Alhamis.

A karshen watan Mayun nan da muke ciki ne Jam’iyyar APC za ta gudanar da zaben fitar da dan takarar shugaban kasarta, tikitin da kusan mutum 25 ke nema a jam’iyyar.

Lawan, wanda dan Majalisar Dattawa ne tun daga 1999, ya ce yana da nagarta da kwarewar da za ta ba shi fifiko a kan sauran abokan fafatawarsa.

“Alhamdulillah an jima ana damawa da mu, tun 2019, muna kuma aiki kafada da kafada da shugaban kasar jam’iyyarmu, Muhammadu Buhari.

“Na san na fahimci yawancin abubunwan da ke faruwa da matsalolin da ke damun kasar nan.

“Fitowarmu takara daga karshe ya isa izina domin ba haka kawai na ce ina son zama shugaban kasa.

“Sai da aka jima kafin wadanda suka ga na cancanta suna neman ni ma in shiga a fafata da ni. Daga baya na amince,” inji shi.