✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ni da Jonathan muka fara rattaba hannu a yarjejeniyar zaman lafiya a zabe – Buhari

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya ce tun kafin lokacin zaben 2015 shi da tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan, suka rattaba hannu a kan yarjejeniyar farko…

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya ce tun kafin lokacin zaben 2015 shi da tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan, suka rattaba hannu a kan yarjejeniyar farko ta zaman lafiya.

Ya ce rattaba wa yarjejeniyar hannu ya taimaka ainun wajen gudanar da zaben 2015 cikin lumana.

Shugaba Buhari ya yi wadannan kalaman ne a wajen shaida yadda ‘yan takarar  Shugaban Kasa a zaben 2023 suka hadu tare da rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya yayin zaben 2023 mai zuwa.

‘Yan takarar sun rattaba hannu kan yarjejeniyar ne ranar Alhamis a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.

Da yake jawabi, Buhari ya ce “Kuna sane da cewa sahihin zabe ba ya samuwa ba tare da zaman lafiya ba.”

Don haka ya yi kira ga masu ruwa-da-tsaki kowa ya yi abin da ya kamata domin a samu a gudanar da babban zaben 2023 cikin nasara da mika ragamar mulki ga zababbiyar gwamnati lami lafiya.

Ya kara da cewa, lokacin da aka tsayar don rattaba wa yarjeniniyar  farko hannu na da matukar muhimmanci duba da an riga an saki hanya don gudanar yakin neman zabe a kasa baki daya.

Haka nan, ya ce  “Muna sa ran ganin rattaba wa kashi na biyu na yarjejeniyar hannu ya zuwa watan Janairun 2023.

Daga nan, Buhari ya yaba wa Kwamitin Zaman Lafiya (NPC) karkashin jagorancin tsohon Shugaban Kasa, Abdulsalam Abubakar, bisa tsare-tsaren da ya sa a gaba.

Kana ya yi kira ga ‘yan kasa da su gudanar da harkokin neman zabe cikin lumana, sannan su guji dukkan abubuwan da ka iya tayar da zaune tsaye.

‘Yan takarar da aka gani wajen rattaba hannun sun hada da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP da Peter Obi na jam’iyyar LP da Rabi’u Musa Kwankwaso na NNPP da kuma Sanata Kashim Shettima, wanda ya tsaya a madadin Asiwaju Bola Tinubu na jam’iyyar APC mai mulki.