Daily Trust Aminiya - ‘Ni na koya wa Ali Nuhu da Adam Zango rawa’
Subscribe
Dailytrust TV

‘Ni na koya wa Ali Nuhu da Adam Zango rawa’

An fi sanin shi da Nazir a cikin Shirin “Dadin Kowa” na tashar Arewa24. Amma sunanshi na asali Ahmed Bello.
Kafin ya zama jarumi a harkar fina-finan Hausa, wato kannywood, Ahmed Bello – wanda aka Haifa a Jos, babban birnin Jihar Filato – mai koyar da rawa ne.
A wannan bidiyon ya bayyana yadda ya koya wa Ali Nuhu da Adam A. Zango, da Sani Danja, rawa.