✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ni ne Mukaddashin Shugaban APC —Gwamnan Neja

Gwamnan Neja ya rantsar da shugabannin APC na jihohi, amma ya ce ba shi da ta cewa game da batun sallamar Buni

Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani Bello, ya sanar cewa shi ne Mukaddashin Shugaban Rikon Jam’iyyar APC na Kasa.
Gwamnan ya bayyana haka ne a hedikwatar jam’iyyar a ranar Litinin, bayan wasu rahotanni da ke cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sallami Shugaban Rikon Jam’iyyar na Kasa kuma Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni, daga mukamin.
Da yake magana bayan taron da ya jagoranta na Kwamitin Rikon Jam’iyyar na Kasa da shugabanninta na jihohi, Gwamna Bello ya ce, “Shugabannin jam’iyyar na jihohi sun karbi rantsuwar mika wuya.”

Ya ce, “Mun tattauna inda aka kwana a shirin babban taron jam’iyya da abin da ya kamata a yi nan gaba domin gudanar da taron na ranar 26 ga watan Maris cikin nasara.”

An tambaye shi dalilin da ya jagoranci taron, sai ya ce, “Ni ne Mukaddashin Shugaba; Na dan jima ina aiki a matsayin riko bayan shugaba (Buni) ya yi tafiya.”

Da aka tambye shi game da gaskiyar batun sallamar Buni daga kujerar, Gwamna Abubakar Sani Bello ya ce, “Ba ni da ta cewa.”

Dambarwar sallamar na zuwa ne a yayin da Buni ke duba lafiyarsa a kasar Jamus, kuma washegarin tafiyar Buhari kasar Birtaniya domin ganin likita.

A ja wa Gwamna Bello kunne

Taron sirrrin da Gwamnan Bello ya gudanar dai ya kasance wani bakon abu a hedikwatar ta APC.

Kafin yanzu,m Sakataren Kwamitin Rikon Jam’iyyar, Sanata John James, ne yake gudanar da harkoki a hedikwatar jam’iyyar bayan tafiyar da Buni ya yi.

Kafin yanzu, shi dai Gwamnan mamba ne kawai a Kwamitin Rikon Jam’iyyar APC.

Neman takara na neman tayar da fitina

Wani mamba a Kwamitin Rikon Jam’iyyar kuma tsohon Mataimakin Sakataren Yada Labaran jam’iyyar, Yekini Nabena, ya gargadi gwamnan da ya dakatar da taron Kwamitin Zartarwar Jam’iyyar (NEC) da ake zargin yana shirin gudanarwa.

Sanarwar da Nabena ya fitar ta yi zargin cewa shirin neman takarar mataimakin shugaban kasa da Bello ke yi na neman kawo kama-karya a jam’iyya.

A cewarsa, wanda mamba ne kawai a kwamitin rikon jam’iyyar ba shi da hurumin yin gaban kana wajen kiran taron.

“Kada Gwamna Bello ya wargaza APC saboda burinsa na zama mataimakin shugaban kasa ko wani abu a 2023; Shi da ire-irensa hankakin siyasa ne da ke cin diddigen jam’iyyar domin kawo kama-karya.

“Ina kira ga jagororin jam’iyya a fadin jihohi da Fadar Shugaban Kasa cewa su taka wa Gwamna Bello burki kan taron Kwamitin Zartar da yake son gudanarwa ba da sanin Mai Mala Buni ko Sakataren Kwamitin Rikon Jam’iyya ba.

“Ai ba shi ba ne Sakatare ko Shugaban Rikon Jam’iyya, to wa ya ba shi ikon kiran irin wannan taron?” Inji Nabena.