✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘”Nigeria Daily” Ne Shirin Podcast Mafi Inganci A Najeriya’

Sashen Yada Labarai ta Intanet na kamfanin Media Trust ne dai yake shirya “Nigeria Daily” da takwaransa na harshen Hausa, “Najeriya A Yau”, a ranakun…

An bayyana “Nigeria Daily” a matsayin na farko a cikin jerin shirye-shiryen podcast na labarai 15 mafiya inganci a Najeriya da suka cancanta a saurare su a 2023.

Wani shafin intanet da ke tace wa mabiyansa shafukan da ya dacewa su bibiya mai suna FeedSpot ne ya bayyana hakan a shafinsa na intanet.

Sashen Yada Labarai ta Intanet na kamfanin Media Trust ne dai yake shirya “Nigeria Daily” da takwaransa na harshen Hausa, “Najeriya A Yau”, a ranakun mako.

Kawo yanzu dai an wallafa shirye-shiryen “Nigeria Daily” guda 398 tun bayan fara shirya shi a watan Yuni na shekarar 2021. 

“Najeriya Daily” shiri ne da ke tsefe batutuwan da suka bayyana a labarai a Najeriya da nufin nuna yadda za su shafi rayuwar al’umma kai-tsaye.

A shafinsa na intanet, FeedSpot, wanda yake da ofishi a Amurka da Indiya, ya ce yana da mabiya wadanda suka yi rajista da shi sama da miliyan 4 a kasashe fiye da 150 na duniya.

Podcast wani sabon tsari ne na yada labarai ta intanet mai kama da rediyo, amma yana bai wa mutum damar sauke ko sauraren shirin da yake son ji a duk lokacin da yake so.