✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Nigeria@62: Yadda matsalolin tsaron Najeriya za su iya zama tarihi – Masana

Masana sun bayyana darusan da Najeriya za ta koya daga kalubalen tsaronta

A ranar Asabar, daya ga watan Oktoban 2022, Najeriya za ta cika shekara 62 da samun ’yancin kanta daga Turawan Mulkin Mallaka na Birtaniya, bayan shafe tsawon shekaru.

Tun daga lokacin zuwa yanzu, kasar ta ga shugabanci iri-iri, daga na mulkin farar hula da na soja tsawon wadannan shekaru.

Sai dai a tsakani, Najeriya ta fuskanci rikice-rikice iri-iri, kama daga na Yakin Basasa na masu neman ballewa da nufin kafa kasarsu ta Biyafara, da rikicin Maitatsine da na addini da kabilanci da kuma na Boko Haram, sai a baya-bayan nan, ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.

Amma babban abin tambaya a nan shi ne wadanne abubuwa ne suka haddasa wadannan rikice-rikicen, wadanne darussa ya kamata a ce Najeriya ta koya tsawon wadannan shekarun, sannan kuma wadanne hanyoyin ya kamata kasar ta bi wajen sake aukuwarsu a nan gaba?

A kan haka ne Aminiya ta tattauna da wasu masana; Ditektib Auwal Bala, wani masanin harkokin tsaro da ke jihar Kano kuma shugaban kamfanin Walewa Securiy Limited da kuma Farfesa Kamilu Sani Fage, masanin harkokin siyasa da dangantakar kasa da kasa, kuma malami a Sashen Kimiyyar Siyasa da ke Jami’ar Bayero da ke Kano (BUK) a kan haka.

Dalilin da Najeriya ta tsallake rikice-rikicen

A cewar Auwal Bala, Najeriya ta samu nasarar tsallakewa tare da yin galaba a kan rikice-rikicen da ta sha fama da su tun daga samun ’yancin kai har zuwa yanzu saboda yadda kafafen yada labarai da malaman addini suka rika wayar da kan mutane.

Ya ce, Wadannan bangarorin sun taka muhimmiyar rawa wajen fadakar da mutane su fahici illar wadannan matsalolin.

Shi kuwa Farfesa Kamilu Fage ya ce daga cikin dalilan, shugabanni da ‘yan siyasar da suke haddasa rigingimun suna yi ne don biyan bukatun kansu, kuma da zarar sun biya sai su janye jikinsu.

Sannan na biyu kuma talakawa su suna harka a tsakaninsu ba tare da bambanci ba. Za ka shiga kungumin daji a Arewacin Najeriya ka iske dan kabilar Ibo ko Bayarabe yana zaune da mutanen wajen ana harka. Haka idan ka je Kudu za ka ga talakawa na harka a tsakanin juna

“Ma’ana dai wadannan rigingimun na masu hannu da shuni ne da’yan boko da kuma manya, ban da talakawa. Shi ya sa wannan din ba ya yin nasara.

“Abu na uku kuma akwai alaka dan zaman cudan-ni-in-cudeka tsakanin bangarorin Najeriya na cinikayya, wacce kowanne yake ganin idan wani ya balle zai samu ’yar wahala a rayuwarshi,” inji Farfesan.

Abubuwa da suka haddasa matsalolin tsaron

Game da abubuwan da suka zama musabbabin kalubalen tsaro a kasar kuwa, masanin ya ce wasu daga cikin ’yan siyasa da dama sun taka mummunar rawa wajen cim ma wasu bukatunsu na kashin kai.

“Musamman ta bangaren tattalin arziki, akwai wasu ’yan siyasar da suke amfana da wadannan matsalolin.

“Sannan akwai bangaren yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa. Sau da yawa wasu sun yi amfani da hanyar saboda idan babu ita, ba za su samu kazaman kudade ba ta kowace hanya.

“Kazalika, yawan jahilci ya taimaka wajen ta’azzara matsalar tsaro. Jahilci ya yi wa mutane katutu. Duk kasar da ake so a gurgunta, harkar iliminta ake gurguntawa, ta yadda ba za ta samu ci gaba da wayewa ba.

“Sannan an yi amfani da rigingimun siyasa don cin zabe, saboda ’yan siyasa ba su yi wa jama’a komai ba,” inji shi.

A nasa bangaren kuwa, Farfesa Fage ya ce irin matsalolin tsaron da ake fama da su yanzu na ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane raunin shugabanci ne yake kawo su.

“Bugu da kari, akwai matsalar kwaikwayo; idan wasu suka yi wani abu suka ga ba a dauki mataki ba, sai su ci gaba. Sannan akwai masu amfana da matsalar ta hanyar samun kudi, ta hanyar hada baki da waus gurbatattun jami’an tsaro,” inji Farfesan.

Darussan da ya kamata Najeriya ta koya

Masanin ya ce akwai dimbin darussa da ya kamata a ce kasar ta koya daga tarin matsalolin tsaron da ta sha fama da su a baya, musamman daga Yakin Basasa.

Ya ce kamata ya yi sauran bangarorin Najeriya su dauki darasi su gane cewa irin wannan yakin babu abin da yake kawowa sai koma-baya.

Auwal Bala ya ce, “Bangaren ’yan Biyafara misali da suka yi yaki, daga karshe sun fahimci wadanda suka zuga su suka fada yakin sun kai su ne sun baro, saboda daga karshe abin kansu ya dawo, su kuma shugabannin nasu sun gudu kasashen waje da nasu iyalan.

“Wanna darasi ne da ya kamata sauran bangarorin Najeriya su dauki darasi daga ciki. Sannan kuma sun ga watakila shi jagoran da yake jagorantar a tayar da kayar bayan ga inda karshensa ya zama, watakila an kama shi an tsare, ko ma kotu tana neman ta yanke masa hukunci,” inji shi.

Najeriya za ta iya magance matsalolin tsaronta na yanzu matukar…

Dangane da matsalolin tsaron da kasar take fama da su yanzu haka na masu tayar da kayar baya da ’yan bindiga da kuma masu garkuwa da mutane domin neman kudin fansa, masanin ya ce akwai abubuwan da matukar aka yi za a iya kawo karshensu.

Ya ce tsarin tsaro yana ka’idoji da dokoki, wadanda idan aka bi su ba a yi musu kara tsaye ba, za a samu sauki.

Daga cikin abubuwan da za a yi ya ce, “na farko shi ne a yi jami’an tsaro masu kula da dazuka, saboda kaso 80 cikin 100 na wadannan laifukan a daji ake aikata su.

“Idan aka yi wadannan dakarun, za a debi mutane ’yan yankin kamar mafarauta da ’yan sa-kai da sauran jami’an tsaro wadanda ba na gwamnati ba, a ba su horo, sai su rika tsare dajin, duk wani motsi da za a yi a ciki suna da masaniya. Idan kasa ta tsare daji, kauye zai samu tsaro. Idan aka samu tsaro a kauye kuma, za a samu tsaro a birni.

“Na biyu kuma a sake wata cibiyar tsaro mai zaman kanta, da za ta rika bincike tana tattara bayanan tsaro. Ba za ta kasance a kan kowacce hukumar tsaro ba, zaman kanta za ta rika yi kamar INEC.

“Za a samar da masana daga bangarorin ilimi daban-daban, su rika hasashen matsalolin da za su faru tun kafin aukuwarsu don a dakile su.

“Abu na karshe kuma ya zama wajibi a yi dokar da za ta haramta biyan kudin fansa. A wurare da dama, a kan yi garkuwa da mutane saboda dalilai daban-daban, amma a Najeriya, saboda karbar kudin fansa kawai ake yi.

“Dalili kuwa shi ne idan suka karbi wadannan kudaden, sukan je ne su sake sayen makaman da za su zo su ci gaba da aikata ta’asar, inji shi.