✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Nijar ta dakatar da bai wa Mali fetur saboda kin mara wa MDD baya

Nijar tana samar da gangar mai kusan 20,000 a kowace rana.

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta dakatar da ba da izinin fitar da fetur zuwa makwabciyarta kasar Mali har sai ta mara wa kokarin da Majalisar Dinkin Duniya ke yi na maido da zaman lafiya kasar baya.

Nijar na daya daga cikin kasashen Yammacin Afirka masu samar da man da kasashen yankin ke amfana da shi, inda take da karfin samar da gangar mai kusan 20,000 a kowace rana.

Majalisar Dinkin Duniya ta shiga Mali ne domin gudanar da shirinta na dawo da zaman lumana a kasar tare da kubutar da ita daga kalubalen masu tsattsauran ra’ayin Islama da take fuskanta.

Ya zuwa hada wannan rahoto duk kokarin da aka yi don jin ta bakin jami’an Mali game da batun hakan ya ci tura.

A matsayin wani mataki na wadata kasar da mai, Nijar ta rage yawan tataccen man da take fitarwa zuwa ketare da kashi 75 a watan Mayu na bana tun bayan tashin da farashin mai ya yi a kasuwar mai ta duniya sakamakon yakin da ya kaure tsakanin Rasha da Ukraine.

(NAN)