✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NIS ta damke ‘yan ci-rani 303 a Akwa Ibom

Hukumar ta sha alwashin tabbatar da tsaro duba da karatowar Zaben 2023.

Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS), ta kama wasu mutum 303 da ake zargin ‘yan ci-rani ne da suka shigo ba bisa ka’ida ba a Uyo, babban birnin Jihar Akwa Ibom.

Kwanturolan NIS a Akwa Ibom, Misis Francisca Dakat, ce ta bayyana haka yayin zantawa da manema labarai a ranar Asabar.

Dakat, ta ce daga cikin bakin haure 303 da aka kama, 285 manya ne yayin da guda 18 kananan yara ne.

Ta ce an cafke bakin hauren ne a wani samame biyo bayan umarnin da hukumar ta bayar na hana bakin haure shiga al’amuran zaben da ke tafe.

Ta ce gabanin kamen, hukumar ta gudanar da taron wayar da kan duk wadanda ba mazauna jihar ba.

“Taron wayar da kai ya gudana a babban birnin Uyo, za a ci gaba da yin irin wannan samamen kuma za a fadada shi zuwa dukkan kananan hukumomin jihar 31.

“An gano daga cikin mutum 303 da suka hannu, akwai guda 100 da suke kasance ‘yan Nijar kuma tuni aka mika su ga mahukuntan da suka dace,” in ji Dakat.

Ta kuma bukaci wadanda ba ‘yan kasar nan ba da su tabbatar sun bi dokar shige da fice ta Najeriya don zama lafiya.

Kwanturolan ta gargadi wadanda ba ‘yan Najeriya ba game da shigowa kasar nan kai tsaye ko a fakaice musamman duba da yadda babban zabe ya karato.

Ta yaba wa Gwamnatin Jihar da sauran jami’an tsaro bisa goyon bayan da suke bayarwa wajen ganin an samu nasarar aiki a jihar.