✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NLC na shirin fara yajin aiki a Filato

NLC ta ce za ta shiga yajin aikin ne domin gargadi ga Gwamanatin Filato kan ta yi abin da ya kama ce ta game da…

Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) da takwararta ta ’yan kasuwa (TUC) a Jihar Filato na shirin fara yajin aikin gargadi na kwana biyar saboda rashin biyan albashi da sauran hakkokin ma’aikata.

Cikin wasikar da ta fitar ranar Alhamis mai dauke da sa hannun shugabanta na jihar, Eugene Manji, NLC ta ce ta soma neman hadin kan sauran takwarorinta a jihar don su shiga yajin aikin.

Shugaban kwamitin sulhu na hadin gwiwa (JNPSNC) reshen Filato, Mista Titus Malau, ya shaida wa NAN cewa shiga yajin aikin ya zama wajibi saboda gazawar gwamnati wajen cimma bukatun ma’aikatanta.

Ya ce matsalar albashin ma’aikata na daga cikin dalilan da suka sanya su yanke shawarar shiga yajin aikin gargadi don jan hankalin gwamnati.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), ya ce NLC ta shirya fara yajin aikin ne ranar 11 ga Disamba da misalin karfe 12:00 na dare.

Shugabannin kungiyar sun yi kira ga ma’aikatan gwamnati a jihar da su ba da cikakken hadin kansu kan matakin.

 

(NAN)