✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

NLC ta bukaci Buhari ya kara wa ma’aikata albashi da kashi 50

NLC ta caccaki gwamnoni kan shawarar sallamar ma'aikatan da suka haura shekaru 50 a duniya.

Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) ta nemi Shugaba Muhammadu Buhari ya kara wa ma’aikata albashi da kashi 50 cikin 100 la’akari da yanayin tsadar rayuwa.

NLC ta bayyana bukatar hakan ne cikin wata wasika da aike wa shugaba Buhari mai dauke da sa hannun shugabanta, Kwamared Ayuba Wabba.

Wasikar ta yi tuni da cewa gwamnonin kasar su suka karfafa batun janye tallafin mai, da kawo batun sallamar ma’aikatan gwamnati da suka haura shekara 50, da kuma rage kudaden da ake bai wa majalisa domin aikin mazabu.

Kungiyar ta caccaki gwamnoni kan wadannan shawarwari, tana mai cewa duk wanda ya goyi bayan ra’ayinsu to ba shi da maraba da makiyin gwamnati.

NLC ta ce batun karin albashi ne abin da ya kamata a mayar da hankali a kai, domin a wannan lokaci shi ne mai muhimmanci.

Masu fafutikar dai na ganin akwai bukatar gwamnati take amfani da yanayin kasa da abubuwan da ke faruwa wajen fayyace albashi da sama wa ’yan kasar sauki.