✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NNPP ta bai wa Kwankwaso tikitin takarar Shugaban Kasa

Mun shiga jam'iyyar NNPP ne don kawo sauyi a siyasar da ake yi ta kama-karya a Najeriya.

Jam’iyyar NNPP ta bai wa tsohon gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso tikitin tsayawa takarar Shugaban Kasa a Babban Zaben 2023.

NNPP ta bai wa Kwankwaso tikitin takarar ne bayan tantace shi da aka yi ranar Talata a Babban Ofishin jam’iyyar da ke Abuja.

Shugaban jam’iyyar NNPP, Farfesa Rufa’i Ahmed Alkali, ya ce sun yi dogon nazari kafin tsayar da Kwankwaso a matsayin dan takararsu.

Wannan ya nuna cewar Kwankwaso zai kara da ‘yan takarar manyan jam’iyyun adawa na APC da PDP.

Tuni wasu jam’iyyun suka gudanar da zaben fitar gwani kamar PDP da ta zabi Atiku Abubakar, yayin da jam’iyyar LP kuma ta tsayar da tsohon gwamnan Jihar Anambra, Peter Obi a matsayin dan takararta.

APC kadai ya rage ta fitar da nata dan takarar, wanda za a fara zaben fid-da-gwaninta a ranar Litinin 6 ga watan Yuni zuwa  9 ga watan Yuni, 2022.

Kwankwaso ya fice daga jam’iyyar PDP bayan ya zarge ta da rashin adalci, wanda hakan ya sa ya sauya sheka zuwa jam’iyyar NNPP mai alamar kayan marmari.

Sai dai tsohon gwamnan na Jihar Kano, a ranar Litinin cikin wata hirar da ya yi a shirin Today’s Politics na gidan talabijin na Channels, ya shaida cewar takararsa ba ta a mutu ko a yi rai ba ce.

Ya ce sun shiga jam’iyyar NNPP ne don kawo sauyi a siyasar da ake yi ta kama-karya a Najeriya.