✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NNPP ta karbi mutum 1000 a Kaduna

’Yan Najeriya sun sha wahala a hannun APC da PDP.

Jam’iyyar NNPP mai alamar kayan marmari ta karbi sabbin mambobi guda 1000 da suka sauya sheka daga jam’iyyun PDP da APC a Jihar Kaduna.

An gudanar da taron karbar bakin ne a Unguwar Hayin Banki da ke Karamar Hukumar Kaduna ta Arewa, inda aka karbi sabbin mambobin har su 1000.

Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban NNPP na mazabar Hayin Banki da Unguwar Kanawa da Farin Gida, Safiyanu Baballe ya ce jam’iyyar ta zo ne domin ta cece ‘yan Najeriya daga rudun da suke ciki.

A cewarsa, ’yan Najeriya sun sha wahala a hannun APC da PDP, wanda hakan ya sa a cewarsa suke da kudurin ganin ‘yan Najeriya sun dara.

A nasa jawabin, daya daga cikin wadanda suka koma NNPP, Hassan Usman Goma, wanda dan takarar Majalisar Jihar ne mai wakiltar mazabar Kawo, ya ce sun koma NNPP ne domin ganin kudirinta na taimakon matasa da sauran ’yan kasa.

Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai dan takarar Majalisai Wakilai a NNPP, Muhammad Ali, da dan takarar Majalisar Jihar Kaduna mai wakiltar Kawo, Magaji Danladi da Sakataren Jam’iyyar NNPP na Jihar Kaduna, Major Yahaya mai ritaya da sauransu.