✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NNPP ta lashe karamar hukumar Shugaban APC na Kano

Da hakan, Abba, wanda shi ma dan asalin Gwale ne, ya kawo karamar hukumarsa.

Abba Kabir Yusuf, dan takarar Gwamnan Jihar Kano, ya yi nasara a zaben Gwaman Jihar Kano, a Gwale, Karamar Hukumar Shugaban Jam’iyyar APC mai mulkin jihar, Abdullahi Abbas.

Baturen zaben, Hafiz Yakasai, ya sanar cewa NNPP ta yi nasara a Karamar Hukumar da kuri’a 39,460, a yayin da APC ke biye da ita da kuri’u 21,548.

Da hakan, Abba, wanda shi na dan asalin Gwale ne, ya kawo karamar hukumarsa.

Yakasai ya kara da cewa, a zaben karamar hukumar, an samu sahihan kuri’u, 64,420, lalatattun kuri’u  928, wanda jimilla ya zama 65,348

Ya kuma bayyana cewa an soke zabe a rumfuna shida da ke yawan masu katin zabe 5,323, sakamakon aringizo da kuma kawo wa tsarin zabe matsala.

An dade ana tayar da jijiyoyin wuya tsakanin APC mai mulkin Jihar Kano, da kuma babbar jam’iyyar adawa ta NNPP.