✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NNPP ta zargi APC da kai wa dan takararta na Gwamna hari a Kano

Rikici tsakanin NNPP da APC a Kano

Jam’iyyar NNPP ta bayyana rashin jin dadinta kan farmakin da ta ce an kai wa dan takararta na Gwamnan a Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf.

NNPP dai na zargin an kai wa Abba harin ne a mazabarsa da ke Chiranci a Karamar Hukumar Gwale tare da bayyana lamarin a matsayin rashin mutunci.

Jam’iyyar ta yi zargin Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Kano, Abdullahi Abbas da wasu ‘yan barandar siyasa ne suka afka masa tare da rera wakokin tunzura al’umma da kuma jifa da duwatsu.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun dan takarar Gwamnan jihar a Jam’iyyar NNPP, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya raba wa manema labarai ya ce, babu wanda ya samu rauni a cikin tawagar dan takarar.

Har ila yau, NNPP ta zargi shugaban na APC da yunkurin tayar da hargitsin da zai kawo rashin zaman lafiya.

Sunusi ya kara da cewa saboda sun ga babu hanyar da za su yi magudi ko bayar da kudi ga masu kada kuri’a shi ya sa ‘yan Jam’iyyar APC suke son tayar da fitina don a barar kowa ya rasa.

Abba Gida-gida ya je mazabarsa ta Chiranci a akwati mai lamba 005 domin kada kuri’arsa, amma ya iske cewa Hukumar INEC ta canza masa wurin zabe zuwa Makarantar Balarabe Haladu.

Abba Gida-Gida ya yi kira ga masu kada kuri’a da su kasance masu bin doka da oda.