✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Norway Ta Bai Wa Manoman Rani 833 Injinan Ban Ruwa A Borno

Kungiyar Tarayyar Turai (EU) da Ma'aikatar Haɗin Kan Tattalin Arziki da Ci Gaban Jamus ne suka dauki nauyin tallafin.

Hukumar Kula da ’Yan Gudun Hijira ta Kasar Norway (NRC) tare da hadin gwiwar Duetsche Gesellschaft fiir Internationale Zusammenarbeit (GIZ) ta Kasar Jamus sun tallafa wa manoma 833 da kayan noman noman rani a Jihar Borno.

A cewar hukumar ta Kasar Norway, rikici na tsawon shekara 13 da illar da COVID-19 ya yi wa tattalin arzikin sun kawo cikas matuka ga hanyoyin rayuwa da bukatun rayuwar al’ummar Borno.

Kodinetan yada labarai na NRC, Samuel Jegede, ya ce an samar wa manoman kayayyakin noman rani ne domin farfado da harkokinsu da suka lalace.

Kungiyar Tarayyar Turai (EU) da Ma’aikatar Haɗin Kan Tattalin Arziki da Ci Gaban Jamus ne suka dauki nauyin tallafin.

Jegede ya ce: “Wannan tallafin an yi shi ne don inganta yanayin magidanta da na al’umma da sana’o’insu lura da yadda tashe-tashen hankula suka haifar da shiga mummunan yanayi a Jihar Borno.

“Kayan aikin gona da ban ruwan da aka samar musu sun kunshi ingantattun iri, takin ruwa, kayan feshi da kayan kariya na ma’aikata da injinan ban ruwa da makamatansu.”

Ya kara da cewa hakan zai bai wa manoma damar samun ruwa duk shekara domin bunkasa noman rani a jihar.

Bayan haka, ya ce NRC ta ba da horo da tallafin tsabar kudi don bunkasa ayyukan samar da kudaden shiga ga manoman.

A cewarsa, kimanin magidanta 840 ne ke sana’ar kiwon dabbobi da sarrafa su da kuma kananan sana’o’i domin samun kudaden shiga.

“Wasu daga cikin manoman sun sami damar yin hayan shaguna tare da sayen kayan aiki da injuna don yin amfani da fasahar da suke da ita wajen dinki, kafinta da gyaran gashi,” in ji shi.

Tonny Villy, Manajan Yanki na NRC, Ofishin Arewa, ya ce NRC ta ba da tallafin abinci ga magidanta akalla 27,287 a cikin shekarar 2021.