✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NPC ta tsayar da ranar kidayar jama’a a Najeriya

Ana kiyasta yawan al’ummar Najeriya ya zarta miliyan 200.

Hukumar Kidayar Jama’a ta Kasa NPC, ta ayyana 29 ga watan Maris mai zuwa a matsayin ranar gudanar da aikin kidayar daukacin jama’a da kuma gidajen da ke fadin kasar.

Shugaban NPC, Nasir Kwarra ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Fadar Gwamnatin Tarayya da ke birnin Abuja jim kadan da kammala ganawa da Shugaba Muhammadu Buhari a wannan Juma’ar.

A cewarsa, nan da 29 na waran Maris zuwa ranar 2 ga watan Afrilu, ma’aikatanmu za su tsinci kansu a fagen kidayar jama’a.

Shugaban na NPC ya ce, za su tabbatar da ingantaccen aikin kidiyar, yana mai cewa, za su kidaya hatta wadanda ba ’yan Najeriya ba da ke zaune a kasar.

A halin yanzu, bayanai na cewa, yawan al’ummar Najeriya ya zarta miliyan 200.