✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NPC za ta dauki mutum miliyan daya saboda aikin kidaya a 2023

Za mu yi amfani da fasahar zamani domin hana 'yan sisaya da 'yan boko yi wa aikin kutse.

Ma’aikatan wucin-gadi akalla miliyan daya ne za a dauka don gudanar da aikin kidayar ‘yan kasa wanda Gwamnatin Tarayya ta shirya gudanarwa a karkashin jagorancin Hukumar Kidaya ta Kasa (NPC) a 2023.

Kwamishina mai wakiltar Jihar Ekiti a hukumar kidayar, Deji Ajayi ne ya bayyana haka, inda ya ce za a yi amfani da fasahar zamani mai inganci wajen gudanar da aikin domin hana ‘yan sisaya da ‘yan boko yi wa shirin kutse.

Ajayi ya bayyana hakan ne Ado Ekiti, babban birnin Jihar Ekiti, a lokacin da yake ganawa da manema labarai a matsayin wani bangare na shirye-shiryen gudanar da shirin kidayar gwaji a jihar.

Ya ce, “Shirin kidaya aiki ne babba wanda ake bukatar ma’aikata miliyan daya wajen aiwatar da shi…”

“Da wannan ne NPC ta yanke za ta kwashi ma’aikata don shirin kidaya na 2023 wanda za a gudanar ta hanyar amfani da fasahar zamani. Shirin kidaya na gwajin da za a gudanar din tamkar wata dama ce ta gwada yiwuwar daukar ma’aikata ta amfani da intet.”

Ya kara da cewa, “Wannan shi ne karon farko da za mu gudanar da shirin kidaya ba tare da amfani da takarda ba, komai zai gudana ne ta amfani da fasahar zamani don kauce wa rashawa da kuma tsabtar aiki don cigaban kasa.

“Kazalika, gwamnati za ta yi amfani da alkaluman da za a samu wajen tsara wa matasa da dalibanmu rayuwa mai inganci da kuma kula da lafiyar ‘yan Najeriya.”

A cewar Kwamishinan, shirin kidaya na gwajin da za a yi jihar zai shafi wasu garuruwa tara ne da suka hada da; liAdo da Emure da Iro da Ijero da Ikole da Iworoko da Ise da Ikun da kuma Omu Ekiti.