✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NPC za ta fara horar da ma’aikata 786,741 da za su yi aikin kidaya

NPC ta ce ma'aikatan za su samu horo kan yadda za su tattara bayanai.

Hukumar Kidaya ta Kasa (NPC), ta ce za ta fara horar da ma’aikata 786,741 tare da tura su wuraren da za su yi aiki a lokacin kidaya da za a gudanar a bana.

Hakan na cikin wata sanarwa da Daraktan Hulda da Jama’a na hukumar, Isiaka Yahaya ya fitar ranar Litinin.

Ya kuma ce adadin zai kunshi masu kididdiga 623,797, sai masu sanya ido 125,944, mataimaka 24,001, Ko’odinetoci 12,000, Manajoji 1,000, masu kula da cibiyoyi 1,639, da masu kula da matakin Kananan Hukumomi 59.

Isiyaka ya ce “A shirye-shiryen gudanar da kidayar yawan jama’a da gidaje na shekarar 2023 da aka tsara za a fara daga ranar 29 ga Maris zuwa 2 ga Afrilu, Hukumar Kidaya ta Kasa ta fara horas da ma’aikatan da za su gudanar da aikin a dukkan jihohi da Babban Birnin Tarayya, Abuja daga ranar Litinin, 23 ga Janairu, 2023.

“An shirya horon ne a mataki-mataki don fara horar da ma’aikatan kidayar jama’a da kuma wadanda za su sanya ido don tabbatar da ingancin bayanan da ake tattarawa.

“Horon ya kunshi koya wa kai darasi, daukar horo ta Intanet, tare da kuma horon da za a gudanar a azuzuwa.”

Yahaya ya kuma ce za a horar da ma’aikatan kan yadda za su cike fom din daukar bayanan jama’a, yadda za su yi mu’amala da mutane yayin aikin da kuma yadda za su nadi bayanan jama’a a komfuta.

“Don tabbatar da cewa bayanan da aka tattara suna da inganci, hukumar ta dauki aiki tare da horar da manajoji da mataimakan inganta bayanai kan yadda za su tantance bayanan da kuma sanya ido kan kidayar,” in ji shi.

Ya kuma yi kira ga masu ruwa da tsaki da su mara wa hukumar baya don gudanar da kidayar cikin nasara.