✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NSCDC ta kwace motoci 300 daga haramtattun matatun mai

NSCDC ta fara bincike kan rundunarta da ke yaki da ayyukan sata da kuma fasa bututun mai

Hukumar Tsaron Farin Kaya (NSCDC) ta ce jami’anta sun kwace motoci 300 da ake amfani da su a haramtattun matatun mai a sassan Najeriya.

Babban Kwamandan NSCDC, Ahmed Abubakar Audi ya ce hukumar ta lalata haramtattun matatun mai 50 tare da cafke mutum 200 a bisa alaka da matatun a chikin shekara guda.

“Matsalar satar mai da fasa bututan mai na karuwa, amma muna kokarin shawo kanta shi ya sa muka kira wannan taro domin lalubo mafita,“ inji shi bayan wani taro da kwamandojin hukumar.

Ya yi bayanin ne bayan zaman da ja jagoranci kwamandojin hukumar da shugabannin sashen yaki da fasa butuun mai domin tsara yadda za a magance matsalar a fadin Najeriya.

Ya ce hukumarsa ta fara gudanar da wani binciken sirri kan rundunarta ta yaki da ayyukan satar mai da fasa bututu a fadin Najeriya.