✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NUC ta ba sabbin jami’o’i masu zaman kansu 12 lasisin fara karatu

Yanzu adadin jami’o’i masu zaman kansu a Najeriya ya kai 111

A daidai lokacin da Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASUU) ke ci gaba da yajin aiki,  Hukumar Kula da Jami’o’i ta Kasa (ASUU) ta ba sabbin jami’o’i masu zaman kansu 12 lasisin fara karatu.

Hukumar dai ta gabatar wa da sabbin jami’o’in lasisin fara aiki ne ranar Alhamis, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito.

Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu ne ya gabatar da takardun ga mamallakan jami’o’in.

Jami’o’in sun hada da Pen Resource da ke Gombe; Al-Ansar da ke Maiduguri; Margaret Lawrence da ke Galilee a Jihar Delta da kuma Khalifa Isiyaku Rabiu da ke Kano.

Sauran sun hada da Sports University da ke Idumuje a Jihar Delta; Baba Ahmed University da ke Kano; Jami’ar Kiwon Lafiya da Fasaha ta Saisa da ke Sakkwato; da kuma Jami’ar Nigerian British University a Aba, a Jihar Abiya.

Akwai kuma Jami’ar Peter University da ke Achina/Onneh a Jihar Anambra; da jami’ar Newgate da ke Minna a Jihar Neja; European University of Nigeria da ke Duboyi a Abuja sai kuma Northwest University da ke Sakkwato.

Da yake jawabi yayin taron, Minista Adamu Adamu ya ce duk da adadin, har yanzu akwai bukatar samun karin wasu jami’o’in a Najeriya.

Ya ce sabbin jami’o’in za su rika aiki kafada da kafada da takwarorinsu tsofaffi wajen ba da horo, wanda zai kasance karkashin kulawar NUC.

Shi ma da yake nasa jawabin, Shugaban NUC, Farfesa Abubakar Adamu Rasheed ya yaba wa wadanda suka kafa jami’o’in, inda ya ce za su kawo ci gaba matuka a Najeriya.

Da wannan sabon adadin, yanzu adadin jami’o’i masu zaman kansu a Najeriya ya kai 111. (NAN)