✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NUC ta sabunta wa darusa 12 lasisin karatu a jami’ar Maitama Sule

Sahalewar za ta fara aiki ne nan take

Hukumar da ke Kula da Jami’o’i ta Kasa (NUC) ta ba jami’ar Yusuf Maitama Sule (YUMSUK) sahalewar nazarin darusa sha biyu da jami’ar ke yi.

Wannan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakinta, Abdullahi Abba Hassan, ya fitar ranar Laraba, inda ya ce sahalewa za ta kare ne nan da shekaru biyar.

Ya kuma ce Daraktan sashin sahalewa ta hukumar Dokta Maryam Sali ce ta sanya hannu kan sakamakon a madadin Sakataren zartarwa na hukumar.

Darussan da jami’ar ta samu sahalewarsu sun hada da Larabci da Ingilishi da Nazarin Addinin Musulunci da kuma Tarihi da Harkokin Kasa da Kasa.

A tsangayar Ilimi kuma, jami’ar ta sami sahalewa a bangaren ilimin Larabci da Tarihi da Kimiyyar Nazarin Halittu da ta Sinadarai da na ilimin Abubuwa Marasa Rai da kuma Nazarin Yanayin Kasa sai ilimin Tattalin Arziki.

To sai dai ya ce bangaren nazarin Hausa ya samu sahalewar wucen gadi da za ta kare a shekara biyu.

Abdullahi ya kuma ce Shugaban jami’ar, Farfesa Hassan Kurawa na kara kaimi a wajen ciyar da jami’ar gaba ta kere saura ta kowanne mataki.