✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Oba na Legas ya koma fadarsa bayan harin EndSARS

Oba na Legas, Rilwanu Akiolu ya koma fadarsa bayan sama da wata biyu ba tare da an yi zama a fadar ba, sakamakon harin da…

Oba na Legas, Rilwanu Akiolu ya koma fadarsa bayan sama da wata biyu ba tare da an yi zama a fadar ba, sakamakon harin da aka kai masa a lokacin zanga-zangar EndSARS da ta haddasa fitintinu.

Oba Akiolu ya isa fadar ta Iga Idunganran ne da yammacin ranar Juma’a cikin kade-kade da raye-raye.

An kai wa fadar sarkin hari ne a ranar 21 ga watan Oktoba, 2020, inda bata-gari suka tarwatsa ma’aikatansa tare da barnata kayayayyki da kuma sace wasu a Fadar.

Daga baya sojoji suka kawo wa Oba Akiolu dauki, suka fitar da shi sakamanon harin da ya tarwatsa fadar.

Tun daga ranar Oban ya koma zama a masaukinsa musanman da ke unguwar Lekki kafin a yi wa fadar gyara.

Yayin da yake shiga fadar an hango Oba Akiolu cikin ado sanye da kayatacciyar farar riga yana rausayawa tare da rangaji sanye da wata jar hula ta sarakuna, inda kai-tsaye ya dangana fadar.

Daruruwan masu fatan alheri da masoya ne suka halarci fadar don kashe kwarkwatar idanunsu.

Masarautar ta ce ta yafe wa dukkan wadanda ake zargi da laifin kai harin ba tare da an dauki kowane irin mataki akansu ba.

Har-ila yau ta yi Allah-wadai da harin, wanda ta bayyana shi a matsayin abun kaico, ta kuma ce wadanda suka dauki nauyin harin za su yi da-na-sanin abin da suka aikata.