✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Obadiah Mailafia karya ya yi min – Shaikh Dahiru Bauchi

Shehin ya ce bai aiki kowa wajen Mailafia yana goyon bayansa yana masa addu'a ba

Shaikh Dahiru Usman Bauchi ya karyata kalaman tsohon Mataimakin Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Obadiah Mailafiya, cewa shehin malamin yana goyon bayansa kuma yana masa addu’a.

Mashahurin malamin na addinin Musulunci ya karyata kalaman ne bayan an sanya masa muryar Mailafia yana magana a cikin wani rahoto na gidan talabijin na Channels, wanda a ciki ya ce yana samun kwarin gwiwa daga al’ummar Musulmi, musamman Shaikh Dahiru Bauchi.

A cewar tsohon Mataimakin Gwamnan na CBN, shehin malamin ya aike masa da cewa yana goyon bayansa kuma yana masa addu’a a kan zargin da ya yi cewa daya daga cikin gwamnonin arewa kwamanda ne na mayakan Boko Haram.

“Wannan magana ba gaskiya ba ce; ni ban aiki kowa wajensa ba a kan wannan batu…

“A da can Mailafia Mataimakin Gwamnan Babban Banki ne lokacin da Sanusi Lamido Sanusi yake rike da mukamin Gwamnan Babban Bankin Najeriya; a wancan lokacin ina tare da su saboda shi Sanusi, kuma ina musu addu’a su yi nasara saboda shi Sanusin; amma in ba wancan lokacin ba ba ma tare kuma ban aiki kowa wajensa ba”, inji Shaikh Dahiru.

‘Ba abin wasa ba ne’

Ita ma Gidauniyar Shaikh Dahiru Usman Bauchi ta yi Allah-wadai da kalaman da Mailafia ya yi kuma ya ambaci sunan shehin malamin a ciki.

Wata sanarwa da lauyan gidauniyar, Barista Aminu Balarabe Isa, ya sanyawa hannu kuma ya raba wa manema labarai, ta nuna damuwa bisa wannan furuci na Mailafia a kan “Jagoranmu, Shugabanmu, kuma Malaminmu, wanda kowa ke girmamawa, ya ce ya na tare da shi kuma ya aika masa da mutane yana masa addua”.

Lauyan ya ce ya kamata Mailafia ya san me yake yi, ya daina kawo sunan shehin cikin sha’anin da ba haka yake ba domin malamin ba abin wasa ba ne.

Ya kara da cewa ya kamata Mailafia ya roki Shaikh Dahiru gafara, kuma ya sani an san girman malamin an san matsayinsa, mutum ne mai fadin gaskiya mai kuma kaunar zaman lafiya.