✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Obasanjo ga ’yan PDP – Ba zan sake dawowa jam’iyyarku ba

Obasanjo ya ce bai ga abin da zai sa ya sake komawa PDP ba.

Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ya ce ba gudu ba ja da baya a matsayin da ya dauka na ficewa daga jam’iyyar PDP da ma harkokin siyasar jam’iyya dungurungum.

Obasanjo, wanda ya taba lashe zaben Shugaban Kasa har sau biyu a karkashin tutar jam’iyyar dai ya fice daga cikinta ne lokacin da ya sami rashin jituwa da tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan gabanin zaben 2015.

A lokacin dai, bayan umartar shugaban jam’iyyar a mazabarsa ya yayyaga katinsa a idon jama’a, Obasanjo ya kuma ce daga ranar ya bar sisayar jam’iyya, ciki har da ta PDP.

Yana wadannan kalaman ne ranar Asabar, lokacin da Shugaban PDP na kasa Iyorchia Ayu da sauran masu ruwa da tsaki na jam’iyyar suka ziyarcesa a Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun.

Iyorchia dai ya jagoranci tsofaffin Gwamnoni da mambobin Kwamitin Zartarwa na jam’iyyar ne don tattaunawa a gidan tsohon Shugaban, wanda yake cikin katafaren dakin karatunsa a birnin na Abeokuta, wajen misalin karfe 12:25 na rana.

Daga cikin tawagar dai akwai tsohon dan takarar Mataimakin Shugaban Kasa a jam’iyyar, Peter Obi da tsofaffin Gwamnonin da suka hada da Sule Lamido na Jigawa da Olusegun Mimiko na Ondo da Liyel Imoke da Donald Duke daga Kuros Riba.

Obasanjo da sauran jagororin jam’iyyar sun yi wata tattaunawar sirri ta sama da sa’a biyu.

Sai dai da yake jawabi jim kadan da kammala tattaunawar, Obasanjo ya ce PDP za ta ci gaba da zama a zuciyarsa kasancewa ya Shugabanci Najeriya har sau biyu a karkashinta.

Ya ce, “Yanzu na daina siyasar jam’iyya, kuma babu abin da zai sa na koma. Duk mai bukatar shawarata don ciyar da Najeriya gaba, a shirye nake da in bayar. Zan ci gaba da zama uban kasa.”

Da yake mayar da martani, Shugaban na PDP ya fada wa Obasanjo cewa, “Ko da ka bar PDP, to jininta ba zai bar jikinka ba.”