✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Obasanjo ya shiga bayan labule da kwamitin sulhu na jam’iyyar PDP

Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo, ya shiga bayan labule tare da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Bukola Saraki a Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun. Tawagar…

Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo, ya shiga bayan labule tare da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Bukola Saraki a Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun.

Tawagar tsohon Shugaban Majalisar Dattawan ta isa babban dakin karatu na Olusegun Obasanjo Presidential Library OOPL da ke birnin Abeokuta da misalin karfe 12.12 na ranar Talata.

Isar tawagar tsohon gwamnan Jihar Kwara ke da uwa kai tsaye suka shiga wata ganawa ta sirri tare da tsohon Shugaban kasar a wani gidan saukar baki da ke harabar OOPL.

A halin yanzu dai Saraki shi ne ke zaman Shugaban Kwamitin Sulhu na jam’iyyar PDP.

Obasanjo wanda ya jagoranci kasar nan daga shekarar 1999 zuwa 2007 a karkashin inuwar jam’iyyar PDP, ya keta katin shaidarsa ta zama dan jam’iyyar gabanin babban zaben kasa na 2015.

Daga bisani Obasanjo ya yi ikirarin cewa ba zai sake jefa kansa a wata jam’iyyar ba kuma ya barranta daga duk wani sha’anin siyasa na kowace jam’iyya.