✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Obasanjo ya tafka babban kuskure kan goyon bayan Peter Obi – Sule Lamido

Ya ce duk da tsohon maigidansa ne, amma ba ya tare da shi

Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, ya ce tsohon Shugaban Kasa, Olusegun Obasanjo, ya tafka babban kuskure kan nuna goyon bayansa ga dan takarar jam’iyyar LP, Peter Obi.

Ya bayyana hakan ne lokacin da ya karbi bakuncin tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar, Ahmad Mahmoud, zuwa jam’iyyar PDP.

Ahmad dai kusa ne a jam’iyyar APC a Jihar, kuma ya taba rike mukamin Mataimakin ne daga shekarar 2007 zuwa 2015, lokacin da Lamidon ya yi Gwamna.

Sai dai da yake zantawa da ’yan jarida a gidansa da ke Bamaina a Karamar Hukumar Birnin Kudu ta Jihar, Sule Lamido ya ce Obasanjo ya kasa fahimtar cewa PDP ce ta mayar da shi duk abin da ya zama.

Sule dai ya taba rike mukamin Minista a zamanin mulkin Obasanjo.

A cewarsa, “Obasanjo ya yi magana ne a matsayinsa na tsohon Shugaban Kasa, kuma PDP ce ta mayar da shi duk abin da yake takama da shi a yau. Shi kuma ga shi ya zo yana ci mata dunduniya.

“Na yarda da Obasanjo maigidana ne, amma kuma shi mutum ne, zai iya yin kuskure, kuma yanzu ma ya tafka shi ta hanyar goyon bayan wanda na da jam’iyyarsa ba, bayan ita ta yi masa riga da wando, har da hula.

“Ko ma me ya faru, ko don maganar karba-karba, wasu mutanen ba su da gaskiya idan an zo yin maganar yin adalci. Lokacin da yake kan mulki, har yunkurin tsawaita wa’adinsa ya yi zuwa karo na uku. Wannan adalci ne?

“Ina girmama shi, amma dole mu tsaya kan akidun jam’iyyarmu na asali. PDP ce ta gina Najeriya zuwa yadda take a halin yanzu.

“Na san ya yanke shawarar goyon bayan Peter Obi ne saboda Atiku da Tinubu nagartattun ’yan takara ne, shi kuma yana shakkar su. Na tabbatar tsoron da yake musu ne yake bibiyar shi,” in ji Sule Lamido.