✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Obiano ya dakatar da sarakunan da suka ziyarci Buhari

An dakatar da sarakuna goma sha biyu da suka ziyarci Shugaba Buhari nan take

Rikici tsakanin masu sarauta da gwamnati ya kara kamari bayan Gwamna Willie Obiano na Jihar Anambra ya dakatar da sarakuna 12 da suka ziyarci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

Gwamnatin Jihar Anambra ta sanar da dakatar da sakarunan ne bisa hujjar rashin neman izimin gwamna Obiano kafi ficewarsu daga jihar domin ziyartar Shugaban Kasa.

“Barin masarautunsu ba tare da sanar da jihar ko kananan hukumominsu ba ya saba dokokin aikinsu. Ko a watan jiya an dakatar da basaraken Masarautar Ukwulu, Igwe Peter Uyanwa kan makamancin wannan laifi” injin gwamnatin jihar.

Takardar da Kwamishinan Kananan Hukumomi da Masarautun jihar, Greg Obi ya fitar a ranar Talata ta ce dakatarwar ta shekara daya ce kuma ta fara aiki ne nan take.

Sanarwar ta soke duk wani mukamin da sarakunnan ke rike da shi gwamnatin jihar da majalisar sarakunan jihar, sannan ta hana su yin duk wani abu a matsayin sarakunan gargajiya.

Ana ganin matakin da gwamnan ya dauka alama ce ta tsananin rashin ga-macijji tsakaninsa da Prince Arthur Eze wanda ya jagoranci tawagar sarakunan a ziyarar da hakarta bai cimma ruwa ba.

Obiano na zargin Sarkin, da jan ra’ayin sauran masu sarautar zuwa Abuja , a yunkurinsa na mayar da Jihar Anambra tamkar a karkashin ikonsa take.

A baya gwamnan ya dakatar da basaraken Masarautar Ukwulu, Igwe Peter Uyanwa, lamarin da ake ganin yana da nasaba da goyon bayansa ga Prince Arthur na kin yarda a mayar da kujerar gwamnan jihar zuwa Anambra ta Kudu.

Gwamnatin na kuma zargin sarakunan da laifin yaba wa Shugaba Buhari kan manyan ayyukan cigaban da yayi a jihar da ma yankin Kudu maso Gabas.

Sarakunan da dakatarwar ta shafa su ne:

  1. Igwe Alex Edozieuno na Mkpunando.
  2. Igwe Mark Anthony Okonkwo na  Alor.
  3. Igwe Chukuwma Bob Vincent Orji na Ezinifite.
  4. Igwe Engr G.B.C Mbakwe na Abacha.
  5. Igwe Chijioke Nwankwo na Nawfia.
  6. Igwe Nkeli Nelly na Igbariam.
  7. Igwe Anthony Onyekwere na Owelle.
  8. Igwe A. N Onwuneme na Ikenga.
  9. Igwe Simon Ikechukwu Chidubem na Umumbo.
  10. Igwe S. O Uche na Ezira.
  11. Igwe Dakta Emeka Ilouno na Ifitedunu
  12. Igwe Peter Ikegbunem Udoji na Eziagulu Otu.