✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ogun ce Jiha ta daya wurin yawan masu cutar AIDS

Sama da mutum 20, 827 ne ke dauke da HIV a jihar Ogun.

Kwamishinar Lafiya a Jihar Ogun, Dakta Tomi Coker, ta ce jihar ta fi kowace jiha yawan masu dauke da cuta mai karya karguwar jiki (AIDS).

Coker ta bayyana haka ne a Abeokuta a bikin ranar masu cutar AIDS ta duniya ta 2020, inda ta ce a jihar akwai masu dauke da cutar sama da 20,827.

Kwamishinar wadda ta samu wakilcin Shugaban Hukumar Asibitocin jihar, Dakta Nafiu Aigoro, ta ce ana dora wadanda suka kamu da cutar akan tsarin magani nan take.

Kwamishinar ta yi kira ga al’umma da su guji tsangwama ko kaurace wa masu dauke da cutar, domin hakan na jefa rayuwarsu cikin mawuyacin hali.

Coker ta ce, a shekarar 1990 aka fara samun mutum na farko da ya  kamu da cutar a jihar.

Ta kara da cewa a yayin da aka yi wa mutum 49,211 gwajin COVID-19, an samu 105 daga cikinsu na dauke da kwayar cutar HIV.

Daga nashi bangaren, Daraktan Hukumar Yaki da Cutar AIDS ta jihar ta Ogun (OGUNSACA) Dakta Kehinde Fatugase, ya ce hukumar na duba yiwuwar samar da kayan gwajin da mutum zai iya yi wa kansa kai tsaye.