✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Okorocha ya ci bugu a hannun basarake

Basaraken ya sa wa Okorocha sanda, sai da ma'aikata suka kwace shi

Tsohon Gwamna Jihar Imo, Rochas Okorocha ya gamu da gamonsa a hannun wani basaken da ya tube a jihar bayan sun yi arba a cikin karshen mako.

Okorocha ya ci bugu a hannun Eze Cletus Ilomuanya ne makonni kadan bayan ya tsinci kansa a caji ofis, sakamakon rikici tsakaninsa da hadimin Gwamna Hope Uzodinma mai ci.

Eze Cletus da Okorocha sun dade suna zaman doya da manja saboda tsohon gwamnan ya tube shi daga kujerarsa na Shuaban al’ummar Obingwu a Karamar Hukumar Orlu ta Jihar.

Duk da umarnin kotu na mayar da Eze Cletus, Okorocha, wanda ya yi jagoranci Jihar Imo daga 2011 zuwa 2019, ya ya ki mayar da basaraken.

Haduwarsu a cikin jirgin sama daga Owerri zuwa Abuja ke da wuya, Eze Cletus ya ce da wa Allah Ya hada shi in ba da Okorocha ba.

Basaraken shi ne Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Imo kuma Shugaban Majalisar Sarakunan yankin Kudu maso Gabas.

Lamarin ya fara kaiwa intaha ne bayan Eze Cletus, wanda kujerarsa ke gefen ta Okorocha a cikin jirgi ya hantari tsohon gwamnan cewa ya tafi ya ba shi wuri.

Kan ka ce kwabo suka shiga cacar bakin da tayar da jijiyon wuya.

Ana cikin haka, sai Eze Cletus ya dauko sandarsa ya fara rafka wa Okorocha, sai da ta kai ga ma’aikatan jirgi sun raba su.

The monarch

Majiyarmu ta ce, bayan haduwarsu a jirgi, sai basaraken ya zargi tsohon gwamnan da cewa bai yi masa adalci ba.

Shi kuma Sanata Okorocha, budar bakinsa ke da wuya, sai ya ce bai yi nadamar saukewar da ya yi wa Eze din ba.

A nan ne fa aka kura ta tashi shugabannin biyu suka yamutsa hazo.

Da yake mayar da martani kan lamarin, kakarin tsohon gwamnan, Sam Onwuemeodo, ya yi zargin Eze Cletus da neman amfani da sa-toka-sa-katsin da ke tsakanin uban gidansa da Gwamna Uzodimna don ya samu shiga a wurinsa.

Sai dai ya bayyana cewa rashin son fitinar maigidan nasa ne ya sa bai yi fada da basaraken ba.