✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Olisa Metuh: Shekara hudu a hanyar zuwa kurukuku

A ranar Talatar da ta gabata ce Babbar Kotun Birnin Tarayya Abuja ta yanke wa tsohon Kakakin Jami’yyar PDP Olisa Metuh daurin shekara 7 a…

A ranar Talatar da ta gabata ce Babbar Kotun Birnin Tarayya Abuja ta yanke wa tsohon Kakakin Jami’yyar PDP Olisa Metuh daurin shekara 7 a kurkuku bayan samunsa da laifin karbar Naira miliyan 400 daga hannun tsohon Mashawarcin Shugaban Kasa, Kanar Sambo Dasuki (mai ritaya), inda aka same shi da laifin cewa babu tabbacin tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ya amince da cire kudaden.

Wannan ne ya kawo karshen tataburzar da aka faro tun a shekara hudu da suka gabata kan shari’ar. Wannan ya sa Aminiya ta rairayo wasu daga cikin muhimman abubuwan da suka faru daga farko zuwa karshen shari’ar.

Shekarar 2016

A ranar 5 ga Janairun 2016 ce EFCC ta gayyaci Metuh ya amsa tambayoyi kan zarginsa da karbar Naira miliyan 400 daga Sambo Dasuki. Sai 15 ga Janairu, Babbar Kotun Birnin Tarayya ta bukaci a ajiye Olisa Metuh a kurkukun Kuje bisa zarginsa da kamfaninsa Destra Inbestiment LTD bisa tuhume-tuhume bakwai. Ranar 19 da Janairun aka bayar da belinsa. A ranar 26 ga Janairu, EFCC ta fara gabatar da shaidu kan zargin da take yi wa Metuh, inda ya gabatar da Nneka Ararume wadda ta bayyana yadda ta taimaka wa Metuh wajen canja masa Dala miliyan 2 sannan ta sanya masa a asusun bankin kamfaninsa.

A ranar 4 ga Fabrairu, Abba Dabo ya bayar da shaida a kotun cewa ya ba EFCC Naira miliyan 25 da Metuh ya ba shi. A ranar 16 ga Fabrairu, Metuh ya nuna ba a yi masa adalci ba idan ba a gayyaci tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ba. A ranar 26 ga Fabrairu, kotu ta ki amincewa da shaidar EFCC cewa Metuh ya jirkita bayanin da ya gabatar.

9 ga Maris, kotu ta yi watsi da tuhumar da Metuh ke yi na EFCC ta rike shi ba bisa ka’ida ba. 17 ga Maris, Babban Alkalin da ke shari’ar ya gargadi wanda ake zargi da kada yi tunanin ba kotu tsoro. Alkalin, Mai shari’a Okon Abang ya yi wannan furuci ne bayan Lauyan Metuh ya kai karar Alkalin wajen Suugaban Babbar Kotun Tarayya yana bukatar a sauya masa alkali, inda ya ce sun yi aji daya da alkalin a makarantar zama kwararren lauya.  24 ga Maris, Metuh ya kawo bukata biyu kotun; daya yana kara nanata bukatar a sauya masa alkali, na biyu a dage sauraron karar domin ba Kotun Daukaka Kara ta kammala sauraron bukatarsa na a dakata a shari’ar. Metuh ya ce yana da dadaddiyar kulalliya da alkali Abang.  28 ga Maris, Alkali Abang ya ce bai san Olisa Metuh kafin fara wannan shari’ar ba.

8  ga Afrilu, kotu ta bukaci Metuh ya fara kare kansa.  11 ga Afrilun, Alkali Abang ya yi watsi da bukatun Metuh hudu na cewa a dakatar da shari’ar, inda ya ce dole Metuh ya gabatar da shaidunsa.

19 ga Mayu, Metuh ya bukaci kotu ta ba shi izinin fita kasashen waje domin ya je Ingila a duba lafiyarsa. 24 ga Mayu, Onyechi Ikpeazu ya ce wanda ya karewa yana kwance a Asibitin Abuja, jikinsa ya yi zafi wanda hakan ya sa bai zo asibiti ba. 25 ga Mayu, kotun ta yi watsi da bayanin Metuh cewa ba ya da laifin komai.  26 ga Mayu iyalan Metuh suka fitar da sanarwar cewa dansu a shirye yake ya mayar da Naira miliyan 400 da ake zargin ya karba daga Sambo Dasuki. 27 ga Mayu, lauyan Metuh ya ce sun rubuta wasika ga EFCC cewa Metuh zai dawo da kudin da ake zargin ya karba.

10 ga Yuni, Metuh bai samu zuwa asibiti ba, inda lauyansa ya gabatar da takarda daga Asibitin Koyarwa na Jami’ar Legas cewa suna lura da lafiyarsa. 30 ga Yuni, Metuh ya ce zai dawo da duk kudin da ake zarginsa da karba domin ya nuna yana tare da yaki da cin hanci da ake yi, sannan ya nuna gaskiyarsa da mutuncinsa.

17 ga Oktoba, Olugbumi Usim-Wilson ya janye daga karbar belin Metuh, inda Metuh ya bukaci canja shi da Ike Ekweremadu.

Shekarar 2017

Ranar 23 ga Fabrairu, kotun ta yi watsi da bukatar Metuh na a kira Sambo Dasuki zuwa kotun.

9 ga Yuni, Kotun Koli ta yi watsi da bukatar Metuh na a sauya masa alkali, inda ta ce Abang ya ci gaba. 30 ga Satumba, kotu ta bukaci Hukumar DSS ta kawo Sambo Dasuki kotu domin ya gabatar da bayani don kare Metuh.  23 ga Oktoba, Dasuki ya bukaci kotu ta jingine bukatar. Sannan Metuh ya sake gabatar da bukatar a kira tsohon Shugaban Kasa Jonathan kotun. 25 ga Oktoba, kotun ta bukaci tsohon Shugaban Kasa Jonathan ya bayyana a gabanta cikin kwana biyar. 30 ga Oktoba, tsohon Shugaban Kasa Jonathan ya ce ba ya da masaniya kan kudin da ake zargin Metuh ya karba. Sannan Jonathan ya ce kotun za ta iya gayyatar Sambo Dasuki domin ya yi musu bayani, bukatar da lauyan Dasuki, Ahmed Raji (SAN) ya nuna rashin yarda, inda ya ce Dasuki ya manta abubuwa da dama saboda ya kwashe shekara biyu a tsare.

Shekarar 2018

12 ga Janairu, Kotun Koli ta yi watsi da karar Metuh cewa Babbar Kotun ba ta damar sauraron karar. 22 ga Janairu, Metuh bai samu zuwa kotu ba saboda rashin lafiya, inda lauyansa ya ce yana kwance a Asibitin Nnamdi Azikiwe da ke Nnewi, Jihar Anambra. 23 ga Janairu, EFCC ta bukaci kotun ta kwace belin da ta ba Metuh saboda kin zuwansa kotu. 25 ga Janairu kotu ta bukaci Metuh ya zo kotu ranar 5 ga Fabrairu ko ta tura shi fursuna, sannan Alkali Abang ya yi watsi da takardar da aka turo masa da asibiti.

5 ga Fabrairu, aka kawo Metuh asibiti kwance a gadon asibiti, wanda hakan ya sa Alkali Abang ya dagr shari’ar. 6 ga Fabrairu, Majalisar Wakilai ta bukaci Babban Lauyan Najeriya, Abubakar Malami ya bar Metuh ya je neman lafiya a kasar waje.  9 ga Fabrairu, Kotun Kolin ta yi watsi da karar Metuh cewa ba ya da laifin komai.

4 ga Mayu, Metuh ya sake gabatar da bukatar a bar shi ya fita kasar waje domin duba lafiyarsa. A 21 ga Mayu, Olisa Metuh ya fadi kasa a lokacin da ya tashi domin shiga wajen amsa tambayoyi. Lauyansa ya sanar da janyewa daga shari’ar, amma alkalin ya ce za a ci gaba da shari’ar. 25 ga Mayu, kotu ta rufe gabatar da shaidun wanda ake zargi

10 ga Yuni, Metuh ya sake bukatar a canja masa alkali, a cire Abang.  2 ga Yuli, Metuh ya bukaci a sake bude damar gabatar da shaidun kare kai, inda ya ce lokacin da aka rufe ba ya kotun. 3 ga Yuli, kotu ta amince domin ya ci gaba da gabatar da shaidun.

25 ga Oktoba, Metuh ya ce ana yi masa hakan ne saboda ya kushe Shugaban Kasa Muhammadu Buhari. 27 ga Nuwamba, Metuh ya zargi EFCC ta rufe masa dukkan asusun bankinsa.

Shekara 2019

30 ga Janairu, kotu ta yi watsi da bukatar Metuh na zuwa kasar wajen asibiti..

5 ga Maris, babban lauyan Metuh, Onyechi Ikpeazu ya gabatar da takardar janyewa daga shari’ar, inda ya ce ‘ana matsa masa da yawa ta gefe’. 13 ga Maris, sabon lauya ya karbi shari’ar.

3 ga Oktoba, Metuh ya kammala gabatar da shaidu. 26 ga Nuwamba, Babbar Kotun Tarayya ta bayyana ranar 25 ga Fabarairun 2020 domin sanar da hukunci bayan kowa ya amince da bayanan da ya gabatar.

Shekerar 2020

A ranar 25 ga watan Fabrairu, wato ranar Talatar da ta gabata, Mai shari’a Okong Abang ya yanke wa Olisa Metuh hukuncin daurin shekara sama da 30, anma zai yi shekara 7, inda ya ce kotu ba ta gamsu cewa tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan yana da masaniya kan kudin da ake zarginsa da karba ba.