Omicron: Mutum 2 sun kamu da sabon nau’in cutar COVID-19 a Najeriya | Aminiya

Omicron: Mutum 2 sun kamu da sabon nau’in cutar COVID-19 a Najeriya

Omicron
Omicron
    Sagir Kano Saleh

Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Kasa (NCDC) ta tabbatar da kamuwar mutum biyu da nau’in Omicron na cutar COVID-19.

Darakta-Janar na NCDC, Dokta Ifedayo Adetifa, ya ce an gano kwayar cutar ce a jikin wasu bakin da suka shigo Najeriya daga kasar Afirka ta Kudu, tun bayan samun labarin bullar sabon nau’in cutar.

“Bayan gudanar da gwaje-gwaje kan baki daga kasashen waje, NCDC a Abuja ta tabbatar da gano mutum na farko mai dauke da nau’in cutar mai suna Omicron.

“Mutum biyun da aka gano suna dauke da ita sun shigo Najeriya ne daga kasar Afirka ta Kudu a makon da ya gabata,” inji shi.

Kasar Afirka ta Kudu ita ce ta farko a nahiyar Afirka da aka samu bullar nau’in cutar, abin da ya sa tuni kasashen duniya suka dakatar da zirga-zirgar zuwa kasar.