✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Osinbajo ya ki ya janye wa Tinubu

Ya jaddada takararsa bayan wasu sun janye wa Tinubu

Mataimakin Shugaban Kasa kuma mai neman takarar shugaban kasa a Jam’iyyar APC mai mulki, Farfesa Yemi Osinbajo, ya ki janye wa uban gidansa, Bola Tinubu, wanda shi ma yake neman takarar.

Osinbajo ya jaddada muradinsa ne bayan mutum bakwai sun sanar da jenya takararsu saboda Tinub.

Ya ce, “A halin da Najeriya take ci, tana bukatar kwararren shugaba, ba wai dan koyo ba; amma idan kuka zabe ni, da ma a shirye nake in fara yi muku aiki.”

“Ni da ma ina gudanar da aikina a matsayin Mataimakin Shugaban Kasa, kuma a shirye nake wa wannan aiki.

“Shi ya sa nake gabatar da kaina ga daliget, domin na riga na shirya wa wannan aiki.”

Ya kuma yi kira gare su da su tabbata cewa abin da za su zaba a zaben fid-da gwanin jam’iyyar ya dace da irin abinda suke rokonda kuma yi wa Najeriya fata a nan gaba.

“Ya ku daliget, idan kuka tashi jefa kuri’a a yau, ku tabbata kuri’arku ta dace da irin makomar da muke roka wa ’ya’yanmun masu tasowa a nan gaba.”

Mutanen da suka janye wa Tinubu a taron sun hada mace daya tilo da ta fito neman tikitn, Barista Oju Ken-Ohenanye, wadda ta bayyana Tinubu a matsayin wanda zai iya ceto Najeriya.

Saunan su ne:

  1. Mace daya tilo, Barista Ken-Ohenanye
  2. Gwamnan Jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar
  3. Gwamnan Jihar Ekiti, Kayode Fayemi
  4. Tsohon Gwamnan Jihar Ogun, Sanata Ibikunle Amosun
  5. Ministan Neja Delta, Godswill Akpabio
  6. Mataimakin Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dattawa, Sanata Ajayi Boroffice
  7. Tsohon Shugaban Majalisar Wakilai, Dimeji Bankole

Mutum daya kuma dan takara mafi karanci shekaru, Felix Nicholas, ya janye wa Osinbajo.

Kawo yanzu, Sauran wadanda za a fafata da su su ne:

  1. Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi
  2. Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello
  3. Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Ahmad Sani Yerima
  4. Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan
  5. Gwamnan Jihar Ebonyi, Dave Umahi
  6. Gwamnan Jihar Kuros Riba, Ben Ayade
  7. Tsohon Gwamnan Jihar Imo, Sanata Rochas Okorocha

Da dai sauransu.