Osinbajo ya tafi wakiltar Buhari a taron ECOWAS a Ghana | Aminiya

Osinbajo ya tafi wakiltar Buhari a taron ECOWAS a Ghana

Osinbajo yayin da zai tafi Ghana
Hoto: Fadar Shugaban Kasa
Osinbajo yayin da zai tafi Ghana Hoto: Fadar Shugaban Kasa
    Ishaq Isma’il Musa

Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya garzaya kasar Ghana domin wakiltar Shugaba Muhammadu Buhari a wani taro na musamman da Kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka wato ECOWAS ta shirya.

Mai magana da yawun Mataimakin Shugaban kasar, Laolu Akande ne ya fitar da wannan sanarwar cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Ya ce tattaunawar da shugabannin Kasashen Yammacin Afirka za su yi a yayin taron da za a gudanar a Accra, babban birnin kasar za ta ta’allaka ne kan batun rikicin siyasar kasar Mali.

Bayani sun ce tawagar mataimakin shugaban kasar ta hada da Karamin Ministan Harkokin Waje na Najeriya Ambasada Zubairu Dada, inda kuma ake sa ran dawowarsu a yau Lahadi.

Ana iya tuna cewa, a Nuwambar bara ne Mista Osinbajo ya ziyarci Accra domin tattaunawa kan wannan batu na siyasar Mali da kuma kasar Guinea.

Daga bisani kuma mai shiga tsakani na Kungiyar ta ECOWAS Goodluck Jonathan ya tafi Mali a ranar 5 ga watan Janairun 2022 domin tattaunawa da hukumomin kasar Mali kan batun tsare-tsaren mika mulki ga farar hula.

A yau ne gwamnatin sojin ta Mali ta ce ta mika sabon tsarin mika mulki ga ECOWAS gabannin soma taronta.