✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Osinbajo zai wakilci Najeriya a jana’izar Sarauniya Elizabeth II

Ana sa ran dawowarsa gida Najeriya a ranar Litinin.

Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, zai wakilci Najeriya a jana’izar Sarauniyar Ingila da za a yi ranar Litinin a Birtaniya.

Mai taimamaka wa Farfesa Osinbajo kan harkokin watsa labarai, Laolu Akande ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar.

Ya ce mataimakin shugaban kasar zai bar Najeriya a wannan Asabar din domin ya hadu da iyalan Gidan Sarautar Birtaniya da Firaiministoci da shugabanin kasashen renon Ingila da sauran shugabannin duniya.

Farfesa Osinbajo na daga cikin manyan bakin da Sarki Charles III zai karbi bakuncinsu a wani taro da za a yi a Fadar Buckingham gobe Lahadi.

Bayanai sun ce Mataimakin Shugaban Kasar wanda ake sa ran dawowarsa Najeriya a ranar Litinin, zai kuma yi wata ganawa da Sakataren Harkokin Wajen Birtaniya, James Cleverly.

A ranar 8 ga watan Satumba ne dai Sauraniya Elizabeth II mai jagorancin Kungiyar kasashe renon Ingila ta riga mu gidan gaskiya.

Sarauniya Elizabeth II wadda ita ce basarakiya mafi dadewa a gadon sarautar Birtaniya, ta shafe shekara 70 a kan karaga, kuma ta mutu bayan shafe shekaru 96 a doron kasa.